Zance Ya Kare: Kwankwaso Ya Gama Yanke Shawara, Zai Bar ADC tare da Peter Obi
- Tsohon 'dan takarar shugaban kasa, Sanata Rabiu Kwankwaso da Peter Obi na shirin ficewa daga ADC zuwa jam’iyyar NDC
- Kungiyar Kwankwasiyya ta bayyana cewa Kwankwaso zai sanar da komawarsa sabuwar jam'iyya watau NDC a makon gobe
- Ana ganin dai rikicin da ke addabar jam'iyyar ADC shi ne babban dalilin da ya jawo Kwankwaso da Obi suka nemi mafita kafin lokaci ya kure
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja – Tsohon gwamnan Kano kuma 'dan takarar shugaban kasa a 2023, Rabiu Musa Kwankwaso, ya shirya ficewa daga ADC zuwa sabuwar jam'iyya da aka kirkiro watau NDC a mako mai zuwa.
Mai magana da yawun kungiyar Kwankwasiyya, Habibu Mohammed, ya shaida cewa sun yanke wannan shawara ne bayan amincewar baki daya daga masu ruwa da tsaki.

Source: Twitter
Da yake hira da The Cable, ya ce tattaunawa da NDC ta kai kusan kashi 90 cikin 100, inda ya kara da cewa ana sa ran Kwankwaso da Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na LP a 2023, za su koma NDC a ranar Litinin ko Talata mai zuwa.
“Ina ganin maigidanmu (Kwankwaso), Peter Obi, da wasu za su koma NDC,” in ji Habibu Mohammed.
'Yan Kwankwasiyya sun dauki matsaya
Jigon na Kwankwaisyya ya bayyana cewa wakilan masu ruwa da tsaki daga dukkan kananan hukumomi 44 na jihar Kano sun taru a gidan Kwankwaso a ranar Juma’a domin yanke hukunci.
Ya ce a karshe sun amince baki daya cewa ya kamata ya sauya sheka zuwa NDC domin shirin tunkarar babban zaben 2027.
Ya kuma kara da cewa Kwankwaso yana Kano a halin yanzu, amma ana sa ran zai dawo Abuja kafin ranar Lahadi gabanin sauya shekar.
Dalilin Kwankwaso na barin ADC
Rahotanni sun nuna cewa rikicin shugabanci a cikin ADC ne ya jawo wannan mataki da Kwankwaso da Peter Obi ke shirin dauka.
A ranar Alhamis, kotun koli ta soke umarnin “kowa ya tsaya a matsayarsa” a rikicin shugabancin jam’iyyar tare da mayar da shari’ar zuwa babbar kotun tarayya domin yanke hukunci.
Hbibu Mohammed ya ce wannan hukunci ya kara nuna rashin tabbas a jam’iyyar ADC, yana mai cewa:
“Idan aka duba shari’ar, za ta dauki lokaci. Har ma za a iya sake daukaka kara. Don haka ba shi da amfani mu ci gaba da zama a can.”

Source: Twitter
Ya kara da cewa dukkan bangaren kungiyar Kwankwssiyya sun amince cewa ya fi dacewa a koma wata jam’iyya da ba ta cikin rikici.
Ya ce sun kuma yi la’akari da sauran jam'iyyun adawa kamar PRP, amma a karshe suka zabi NDC, kamar yadda Punch ta kawo.
Kwankwaso ya gana da shugabannin NDC
A wani labarin, kun ji cewa tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya karɓi shugabannin jam'iyyar NDC a Abuja.
An ruwaito cewa daga cikin waɗanda suka halarci ganawar akwai Mohammed Bakin, mataimakin shugaban NDC na ƙasa na shiyyar Arewa maso Yamma.
Duk da babu wata sanarwa a hukumance daga bangarorin biyu game da cikakken abin da suka tattauna, amma majiyoyi sun ce jigan-jigannsun duba yiwuwar haɗin gwiwa.
Asali: Legit.ng

