Abinda ya kamata ku sani game da sabon gwamnan Gombe, Inuwa Yahaya

Abinda ya kamata ku sani game da sabon gwamnan Gombe, Inuwa Yahaya

A ranar Asabar 9 ga watan Maris ne Hukumar zabe ta Najeriya INEC ta gudanar da zabukkan gwamnoni da 'yan majalisun jiha a wasu jihohin kasar. An gudanar da zaben cikin lumana a mafi yawancin johohi duk da cewa akwai wasu jihohin da aka samu matsaloli da su kayi sanadiyar rashin soke zabukkan ko jinkirin fadin sakamakon.

Daya daga cikin johohin da aka kammala zabe cikin lafiya har ma aka sanar da wanda ya lashe zaben itace jihar Gombe.

A jihar ta Gombe dan takarar jam'iyyar All Progressives Party, APC, Inuwa Yahaya ne ya lashe zaben gwamna da kuri'u 364,179 inda ya doke abokin hammayarsa, Sanata Usaman Nafada na jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP da ya samu kuri'u 222,868.

Abinda ya kamata ku sani game da sabon gwamnan Gombe, Inuwa Yahaya
Abinda ya kamata ku sani game da sabon gwamnan Gombe, Inuwa Yahaya
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Bidiyon yadda Gwamna Bello ya yi murnar lashe zabe cikin sabon salo mai kayatarwa

Kasancewarsa sabon gwamna ne yasa Legit.ng ta kawo wasu muhimman abubuwa da ya kamata ku sani a kan zababen gwamnan na jihar Gombe, Inuwa Yahaya.

1. An haifi Inuwa Yahaya ne a ranar 9 ga watan Oktoban 1961 a garin Jekadafari a jihar Gombe

2. Ya yi karunta fannin akanta a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria inda ya kammala a shekarar 1983.

3. Daga bisani ya karo ilimi ta hanyar yin kwasakwasai a fannin akanta a ma'aikatar State Investment & property development da ke Bauchi.

4. Bayan hakan, ya koma kamfanin Nasara motors inda ya zama manajan gudanarwa da hada-hadar kudade na kamfanin.

5. Inuwa ya tsindumma cikin harkar siyasa a shekarar 2003 a lokacin mulin Danjuma Goje inda ya zama kwamishinan kudi da cigaban tattalin arziki na jihar inda ya shafe fiye da shekaru 7 a matsayin kwamishina.

6. Daga bisani ne ya yi takarar gwamna karkashin jam'iyyar APC kuma ya yi nasarar lashe zabe.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel