Rashin kammala zabe: Mata sama da 1000 sun yi zanga zanga a ofishin INEC dake Sokoto

Rashin kammala zabe: Mata sama da 1000 sun yi zanga zanga a ofishin INEC dake Sokoto

Sama da mata 1000 ne suka yi zanga-zanga a ranar Talata, 12 ga watan Maris a Ofishin INEC da ke Sokoto inda suka bukaci hukumar da ta bayyana Tambuwal a matsayin zababben gwamnan jihar ba tare da bata lokaci ba.

Matan sun nemi dalilai da yasa INEC ta yanke shawaran dage zabe da Tambuwal ya lashe a matsayin ba kammalalle ba.

Yayin da yake magana a madadin mata masu zanga-zangan, Farfesa Aisha Madawaki, da Dakta Kuku Haruna, Kulu Sifawa tare da shushugaban matan, Rabi Gayawa sun bayyana cewa sun kasance a ofishin INEC don kaddamar da bakin cikinsu bisa zaben gwamnoni da aka gudanar a ranar Asabar wanda suka yi ikirarin sun lashe sannan aka bayyana a matsayin ba kammalalle ba.

Rashin kammala zabe: Mata sama da 1000 sun yi zanga zanga a ofishin INEC dake Sokoto
Rashin kammala zabe: Mata sama da 1000 sun yi zanga zanga a ofishin INEC dake Sokoto
Asali: UGC

A cewar mata masu zanga-zangan, Gwamnatin Tarayya wacce jam’iyyar APC ke jagoranta tare da hukumar INEC suna juya zabbukan da PDP ta lashe tun daga 2015 a matsayin zabbuka da ba kammalallu ba.

Yayinda take ba da dalilin da yasa suka fito zanga-zangan kwansu da kwarkwatan su, wata mamba na hukumar makarantun Firamare wato State Universal Basic Education Board (SUBEB) Hajiya Fatima Illo tace babu gwamna a Najeriya dake da zuciyar shugabanci irin na Tambuwal.

KU KARANTA KUMA: Zabe: Yadda ‘yan ta-more suka kasha ‘yan sanda biyu a Sokoto – Kwamishina

Yayin da take bada goyon bayan ikirarin ta, Illo ta ce a tarihin Najeriya, gwamna Aminu Taambuwal ne kadai ne ya san martabar mata tunda har ya zabi mata uku a matsayin kwamishinoni, 4 a matsayin masu bada shawara na musamman, 6 a matsayin manyan darektoci,3 a matsayin mambobi sannan 69 a matsayin kansiloli duk a jihar.

Matan sun ce a shirye suke don cigaba da gudanar da zanga-zangan a kulla yaumin har sai hukumar INEC ta bayyana Aminu Waziri Tambuwal a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnoni da aka gudanar a ranar Asabar a jihar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel