Dan takarar gwamnan APC na jihar Taraba, Sani Danladi zai garzaya kotu
- Dan takarar gwamna na APC a Taraba, Sani Danladi ya ce bai yarda da sakamakon zaben gwamna da INEC ta sanar a jihar ba
- Danladi ya yi ikirarin cewa an tafka muguwar magudi a sassan jihar inda a wasu wuraren aka rika yiwa magoya bayan APC barazana
- Danladi ya ce zai garzaya kotu domin a kwato masa nasararsa da jam'iyyar PDP mai mulki a jihar ta kwace da karfi
Dan takarar gwamna na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Taraba, Sani Danladi Abubakar ya ce zai kallubalanci sakamakon zaben da aka gudanar ranar Asabar da ta gabata inda hukumar INEC ta ce sanar da cewa gwamna mai ci, Darius Ishaku ne ya lashe zaben.
Ya ce an tafka magudi da rashin bin ka'idojin zabe a yayin gudanar da zaben na gwamna a jihar na Taraba.
DUBA WANNAN: 'Yan bindiga sun kai hari caji ofis, sun kashe DPO da 'yan sanda 3 a jihar Edo
Danladi ya yi ikirarin cewa ba ayi amfani da na'urar tantance masu zabe ba a garuruwan Zing, Yorro, Kurmi, Takum da Wukari.
Ya kuma kara da cewa an rika yiwa magoya bayan jam'iyyar APC barazana da tsorata su wanda hakan ya hana su samun damar kada kuri'a a garuruwan Takum, Wukari, Kurmi da Ussa inda ya ce an rubuta sakamakon zaben ne ba tare da amfani da na'urar Card Reader ba a wurare da dama a jihar.
Dan takarar gwamnan na APC ya ce bai amince da sakamakon zaben ba baki daya kuma zai garzaya kotu domin ya kwato nasararsa da jam'iyyar PDP mai mulki a jihar ta sace.
Idan ba a manta ba, wakilan jam'iyyar APC ba su saka hannu a kan sakamakon zaben gwamna ba da baturen zabe na jihar, Farfesa Adamu Iya ya sanar ba a garin Jalingo.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng