'Me Ka Tsinana a Shekaru 4': Malamin Addini Ya Kalubalanci Tazarcen Tinubu
- Babban malamin coci, Johnson Suleman ya soki shirin Bola Tinubu na neman wa’adi na biyu a 2027 a Najeriya
- Faston ya bayyana cewa gwamnati ta gaza magance tsaro, tsadar rayuwa da matsalar wutar lantarki a fadin kasar
- Suleman ya ce aikin gwamnati shi ne mafi kyawun yakin neman zabe, yana zargin cewa shugabanni suna lalata adawa saboda gazawar da suka yi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Auchi, Edo - Fasto kuma babban mai kula da cocin Omega Fire Ministries International, Johnson Suleman, ya kalubalanci tazarcen Bola Tinubu.
Fasto Sulaiman ya tambayi dalilin da ya sa Shugaba Bola Tinubu ke neman wa’adi na biyu duk da matsalolin kasar.

Source: Twitter
Premium Times ta ruwaito cewa gabanin zaben shugaban kasa na 2027, gwamnoni da manyan jiga-jigan APC daga jihohi daban-daban sun bayyana goyon baya ga Tinubu.
Malamin ya yi wadannan kalamai ne yayin wani wa’azi a Auchi da ke Edo, inda ya gabatar da huduba mai taken “Power to Get Wealth”.
Fasto ya soki salon mulkin Tinubu
Faston mai shekara 55 ya ce halin matsin tattalin arziki da rashin tsaro da ake ciki ya kamata su sa mutane yin tunani sosai kan neman wa’adi na biyu na Tinubu.
Suleman ya ce idan shugabanni sun hau mulki ta hanyar magudi, ya kamata jama’a su san cewa an yi magudin kuma hukuncin Allah zai hau kansu.
Ya ce idan shugaba ya kasa yin aiki a wa’adin farko, babu dalilin da zai sa a sake zaben sa domin wa’adi na biyu a gwamnati.
Faston ya ce aikin gwamnati shi ne mafi kyawun yakin neman zabe, yana zargin gwamnati da lalata adawa saboda ta gaza yin abin kirki ga jama’a.
Ya ce farashin dala ya tashi daga N460 zuwa N1,500 yayin da farashin mai da sauran kayayyaki suka kara jefa mutane cikin wahala mai tsanani.
Suleman ya bayyana cewa ba yanzu ya fara sukar gwamnati ba, yana cewa ya taba sukar gwamnatin Goodluck Jonathan lokacin sace daliban Chibok a baya.

Source: Facebook
'Abin da ya kamata gwamnatin Tinubu ta yi'
Malamin ya ce idan gwamnati ba za ta iya magance duk matsaloli ba, ya kamata ta samu nasara a kalla a bangare guda domin jama’a.
Ya ce idan gwamnati ta kasa samar da wutar lantarki, to ta samar da tsaro ko saukin rayuwa domin rage wahalar talakawan Najeriya.
Ya ce har yanzu gwamnatin ta gaza wajen kare rayukan jama’a yayin da sace-sacen mutane da yunwa ke ci gaba da addabar Najeriya sosai.
Suleman ya nuna fatan cewa wata rana Najeriya za ta zama kasa mai aminci inda mutane za su rika tafiya cikin dare ba tare da tsoro ba.
Ya ce Allah zai tayar da shugabanni masu kishin kasa da za su yi mulki cikin gaskiya da sadaukarwa domin cigaban al’umma baki daya.
Fasto ya yi hasashen zaben Tinubu
Mun ba ku labarin cewa fitaccen fasto, Samuel Ojo, ya ce yunkurin ‘yan adawa na hana Shugaba Bola Tinubu yin tazarce a zaben 2027 ba zai yi nasara ba.
A cewarsa, Ubangiji ya riga da ya rubuta nasarar Tinubu a 2027, don haka, ko ana ha maza ha mata, Tinubu ne mai nasara a zaben.
Ojo ya yi gargaɗi ga 'yan adawa da su hakura da 2027, domin Ubangiji bai gama amfani da Tinubu ba, akwai sauran aiki a gabansa.
Asali: Legit.ng


