Annoba: Jerin sunayen yara 41 da aka ceto a rubzawar ginin makaranta a Legas

Annoba: Jerin sunayen yara 41 da aka ceto a rubzawar ginin makaranta a Legas

Akalla kananan yara 41 sun tsallake rijiya da bayan a rubzawar ginin makarantar firamaren Ohen dake Ita Faji, Legas. Legit.ng tana iya tabbatar muku.

Jerin sunayen yaran da jaridar Sahara Reporter ta samu a ranar Laraba ya kunshi sunayen dalibai 41 da kuma wasu biyar da ba'a gano sunayensu ba. Dukkansu na cikin koshin lafiya.

Daga cikin yaran da suka tsira akwai yan mata 22, maza 17 da kuma wasu biyu da ba'a bayyana jinsu ba.

Akwai malamai biyu, wasu manya uku, yayinda sauran talatin da shidan kananan yara ne.

Akalla mutane 12, wanda ya kunshi kananan yaran makaranta sun rasa rayukansu, amma har yanzu ana fito da wadanda suka rage a cikin rusassahen gini kuma adadin wadanda suka mutu na iya karuwa.

Da safe mun kawo muku rahoton cewa wani makaranta gini mai hawa ukku da ke yankin Itafaji, tsibirin Legas ya rubza a ranar Laraba, lamarin da ya haddasa tashin hankali da rudani tsakanin al'ummar da ke zaune a kusa da ginin.

Channels TV ta ruwaito cewa akwai wata makarantar Firamare da ke a hawa na ukku na ginin, inda ake tsammanin daliban makarantar sun mutu, yayin da wasu har yanke ke a cikin ginin ba tare da samun hanyar fita ba.

Ga jerin:

Annoba: Jerin sunayen yara 41 da aka ceto a rubzawar ginin makaranta a Legas
Annoba: Jerin sunayen yara 41 da aka ceto a rubzawar ginin makaranta a Legas
Asali: Facebook

Asali: Legit.ng

Online view pixel