Jami’an Gwamnatin Trump 5 da Yakin Iran, Isra’ila Ya Jawo Suka Bar Kujerunsu

Jami’an Gwamnatin Trump 5 da Yakin Iran, Isra’ila Ya Jawo Suka Bar Kujerunsu

Shugaba Donald Trump ya rasa wasu manyan jami’an gwamnatinsa biyar tun bayan fara yakin Amurka da Isra’ila da Iran

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Washington DC, US - Yayin da ake ci gaba da yaki tsakanin Iran da Isra'ila, wasu Amurkawa na nuna rashin amincewa kan rikicin.

Wasu ministoci sun bar Majalisar zartarwa a gwamnatin Donald Trump da shugabancin sojojin Amurka tun bayan fara yakin Iran.

Wasu sun bar kujerunsu a gwamnatin Amurka kan yaki da Iran
Jagoran addini a Iran, Mojtaba Khamenei da Shugaba Donald Trump na Amurka. Hoto: Donald J Trump, Iran Military Media.
Source: Facebook

Shugaba Donald Trump da Ministan tsaro Pete Hegseth sun jagoranci korar wasu ministoci da manyan shugabannin soja a watannin bazarar bana, cewar Washington Post.

Korarren sakataren rundunar ruwa John Phelan ya bar mukaminsa bayan watanni 13, yayin da gwamnatin Trump ke fuskantar rikice-rikice da ficewar manyan jami’ai.

Jami'an da suka bar gwamnatin Donald Trump

Tun daga watan Maris, 2026 akalla manyan jami’ai biyar aka tilasta masu sauka daga mukamansu ko suka yi murabus saboda matsin lamba daga gwamnati.

Kara karanta wannan

Iran ta yi magana, da yiwuwar yaki ya kuma barkewa tsakanin kasar Musulunci da Amurka

Wannan sauyi ya zo ne lokacin da yakin Amurka da Isra’ila da Iran ya jawo matsala, tashin farashin makamashi da faduwar karbuwar Trump.

Legit Hausa ta yi duba game da jerin jami’an da suka rasa kujerunsu a gwamnati da kuma dalilan ficewarsu.

1. Sakataren Rundunar Ruwa, John Phelan

John Phelan ya bar mukaminsa da ya dade yana rike da ita, kamar yadda ma’aikatar tsaro ta Pentagon ta sanar ana cikin yaki da Iran.

Mai magana da yawun Pete Hegseth mai suna Sean Parnell ya ce sakataren rundunar ruwa ya bar Pentagon bayan watanni 13 a aiki.

Wakilin Legit Hausa ya ruwaito cewa gwamnati ta ce an bukaci attajirin da ya tara kudin yakin neman zaben Trump ya sauka.

Majiyoyi biyar sun shaida cewa Phelan ya yi ta rikici da Hegseth kan yadda yake tafiyar da aikin gina jiragen ruwa.

Jami'in gwamnatin Trump ya bar kujerarsa
Donald Trump a hagu, John Phelan a gefen dama. Hoto: @SECNAV|Getty Images.
Source: Twitter

2. Babban Hafsan Sojoji, Janar Randy George

Janar Randy George ya yi ritaya daga mukaminsa a wannan watan yayin da yakin Iran ke ci gaba da daukar hankali.

An yi hasashen zai ci gaba da zama har zuwa shekarar 2027, amma Pete Hegseth ya bukaci ya sauka daga mukaminsa.

Kara karanta wannan

Zambar N1.5bn: Gwamnatin Kano za ta hukunta jami'an da suka tsakure albashin ma'aikata

Jami’an tsaro sun bayyana cewa an kuma cire Janar David Hodne da Manjo Janar William Green Jr. daga mukamansu ba tare da bayyana dalili ba.

Ficewar George ya bai wa Hegseth damar sake tsara kwamitin hafsoshin soja da ke bai wa shugaban kasa da ministan tsaro shawara.

Ana zargin minista da raba hafsan sojoji da kujerarsa
Ministan tsaron Amurka, Pete Hegseth yayin jawabi a Washington. Hoto: @pete_hegseth.
Source: Twitter

3. Babbar Lauyar Kasa, Pam Bondi

Pam Bondi ta bar mukaminta a wata Afrilun 2026 bayan watanni 14 tana jagorantar ma’aikatar shari’a ta Amurka.

Trump ya bayyana Bondi a matsayin “babbar mai kishin Amurka kuma aminiya,” yana cewa za ta koma wani muhimmin aiki a bangaren masu zaman kansu.

Rahotanni sun ce Trump ya nuna rashin jin dadi kan jinkirin Bondi wajen bin abokan hamayyarsa ta fuskar shari’a.

An maye gurbinta da Todd Blanche, tsohon lauyan Trump, har sai an tabbatar da sabon wanda zai karbi mukamin.

4. Ministar Kwadago, Lori Chavez-DeRemer

Ministar kwadago Lori Chavez-DeRemer ta yi murabus domin komawa aiki a bangaren masu zaman kansu kamar yadda Fadar White House ta sanar.

Murabus din ya biyo bayan matsin lamba daga zarge-zargen rashin da’a wajen tafiya da kudin gwamnati domin bukatun kai duk da wasu na danganta hakan da yakin Iran.

Kara karanta wannan

Amurka ta tafka asara a yaki da kasar Musulunci ta Iran, ta kashe kimanin Dala biliyan 25

Lauyanta Nick Oberheiden ya ce ta sauka ne domin kada binciken ya hana ma’aikatar kwadago gudanar da ayyukanta yadda ya kamata.

Mai magana da yawun White House Steven Cheung ya ce mataimakinta Keith Sonderling zai zama mukaddashin shugaban ma’aikatar.

Ministar kwadago ta bar gwamnatin Trump
Lori Chavez-DeRemer da Shugaban kasar Amurka, Donald Trump Hoto: Win McNamee, Andrew Harnik.
Source: Getty Images

5. Ministar Tsaron Cikin Gida, Kristi Noem

Donald Trump ya sanar a watan Maris, 2026 cewa zai maye gurbin Kristi Noem da Sanata Markwayne Mullin a ma’aikatar tsaron cikin gida.

An mayar da ita wata sabuwar kujera mai suna “Jakadiyar Musamman ta Garkuwar Nahiyar Amurka” domin kula da tsaro a yankin yammacin duniya.

Sauyin ya biyo bayan suka masu yawa kan yadda take tafiyar da shirin korar bakin haure daga Amurka, cewar Al Jazeera.

Hatta wasu ‘yan jam’iyyar Republican sun nuna shakku kan dacewarta da mukamin da take rike da shi.

Babban hadiminta Corey Lewandowski, wanda ya taba aiki tare da Trump kafin a taba korarsa, shi ma ya bar ma’aikatar a watan guda.

Nukiliya: Mojtaba Khamenei ya caccaki Amurka

A baya, mun ba ku labarin cewa jagoran addin a Iran, Ayatollah Mojtaba Khamenei ya yi magana game da shirinta na nukiliya a kasar.

Kara karanta wannan

An fitar da hotunan bindigogi da wukaken da aka so kashe Trump da su

Khamenei ya ce Iran ba za ta mika shirinta na nukiliya da makamai masu linzami ba, duk da matsin lambar Amurka.

Ya zargi Amurka da tsoma baki a yankin Gulf, yana mai cewa Iran za ta ci gaba da kare muradunta duk rikicin da ake ciki.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.