Da duminsa: Kungiyar Boko Haram (ISWAP) ta barke gida biyu

Da duminsa: Kungiyar Boko Haram (ISWAP) ta barke gida biyu

Da alamun an samu baraka cikin gidan yan kungiyar tada kayar bayan Boko Haram, sashen daular Islama a yankin Afrika maso yamma wato ISWAP, bayan yaduwan labarin sauke shugabanta Abu Mus'ab Albarnawi.

Legit.ng Hausa ta samu wannan rahoto daga shahrarren dan jarida, Ahmad Salkida, inda ya bayyana cewa lallai an samu baraka a cikin yan kungiyar amma har yanzu ba'a wacce bangare ke da goyon bayan kungiyar ta duniya ba.

Yace: "Ingantaccen labarin da ke iso min yanzu na nuna cewa an samu rabuwar kai a cikin kungiyar daular Islama a yankin Afrika maso yamma wato ISWAP. Abinda bai bayyana ba yanzu shine, shin wace bagagare ke da goyon bayan kungiyar ta ISIS."

"Abin sha'awar shine, Abu Musab ne wanda ya alanta saukesa daga mulkin kungiyar a wata faifan rediyo. Shin ya yi wannan sanarwan cikin tsoro ne? Me yasa ISIS ta dunia bata furta komai kan rikicin shugabancin ba duk da cewa wannan na daga cikin wakilanta mafi karfi."

KU KARANTA: ISWAP ta tsige Albarnawi, ta nada sabon shugaba

Abu Mus'ab Albarnawi ya zama shugaban ISWAP ne bayan ya kafa tsagin kungiyar Boko Haram, lamarin da ya jawo batawar sa da Abubakar Shekau, shugaban kungiyar Boko Haram bayan mutuwar Muhammad Yusuf, shugaban kungiyar na farko.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel