Matar Abdulsalami ta yi magana a kan yiwuwar mulkin mace a Najeriya

Matar Abdulsalami ta yi magana a kan yiwuwar mulkin mace a Najeriya

Uwargidar tsohon Shugaban kasa, Justis Fati Lami Abubakar ta caccaki tsarin ci gaban siyasar kasar sannan ta kaddamar da cewar kasar Najeriya tayi rikan da ya kamata a samu wata shugaba mace.

A wata hira da tayi da jaridar Vanguard a Minna, babbar birnin jihar Niger, Justis Fati wacce ta kasance uwargidar tsohon Shugaban kasa, Janar Abdulsalami Abubakar, tace duba ga irn muhimman rawar gani da mata ke takawa a mulkin kasar a dukkan matakai na gwamnati kama daga kananan hukumomi, jihaa da kuma tarayya, “ya nuna cewa Najeriya ta rika, akwai mata da dama da za su iya tafiyar da al’amuran kasar.”

Matar Abdulsalami ta yi magana a kan yiwuwar mulkin mace a Najeriya
Matar Abdulsalami ta yi magana a kan yiwuwar mulkin mace a Najeriya
Asali: Facebook

Misis Abubakar wacce ta kasance mace ta farko da ta riki mukamin Shugaban alkalai a jihar Niger tace: “Ashirye matan Najeriya suke da su kai kasar zuwa matakin ci gaba. Ina iya fada kai tsaye cewa matan kasar nan sun shirya ma komai."

Kan ko kasar na da matan da za su iya shugabanci, Fati tace: “Kada ma ku yi Magana akan iyawar mata saboda muna dasu da yawa. Suna a ko ina birji sannan kuma a shirye suke suyi shugabanci mai kyau.

KU KARANTA KUMA: Zabe: Yadda ‘yan ta-more suka kasha ‘yan sanda biyu a Sokoto – Kwamishina

“Abunda ya rage masu kawai shinelokaci da samun dama, wanda suna da matkar muhimmanci wajen shugabanci sannan kuma ina da yakinin cewa lokacin ya kusa."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel