14 daga cikin 'yan majalisar dokokin jihar Zamfara 24 sun fadi zabe

14 daga cikin 'yan majalisar dokokin jihar Zamfara 24 sun fadi zabe

'Yan majalisun dokokin jihar Zamfara 14 cikin 24 ba za su koma majalisar ba kamar yadda kamfanin dillancin labarai na kasa NAN ya ruwaito.

NAN din ta kuma ce 9 cikin 'yan majalisun 24 za su koma majalisar yayin da kakakin majalisar, Sanusi Rijiya zai wuce majalisar wakilai na tarayya ne kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Wadanda ba za su koma majalisar ba sun hada da mataimakin kakakin majalisa, Muhammad Abubakar, Bulaliyar Jam'iyya, Abdullahi Dansadau, mataimakin bulaliya, Malam-Mani Malam-Mummuni, Abubakar Ajiya da Hashimu Shehu Gazura.

DUBA WANNAN: Abinda ya kamata ku sani game da sabon gwamnan Gombe, Inuwa Yahaya

14 daga cikin 'yan majalisar dokokin jihar Zamfara 24 sun fadi zabe
14 daga cikin 'yan majalisar dokokin jihar Zamfara 24 sun fadi zabe
Asali: UGC

Saura sun hada da Salisu Musa, Bello Fagon, Shehu Ibrahim, Muazu Faru, Mansur Muhammad Dambala, Lawali Dagonkade da Abu Dahiru.

Dukkan 'yan majalisun dokokin 14 sun sha kaye ne bayan jam'iyyar ta APC ta nada su takara a maimakon gudanar da zaben fidda gwani a jihar.

A wani bangaren, 'yan majalisa 9 da su kayi takara kuma su kayi nasarar lashe zabe sun hada da shugaba a majalisa, Isah Abdulmumin, mataimakinsa, Bello Maiwurno, Aliyu Ango-Kagara, Abu Ibrahim-Maru, and Ibrahim Kwatarkwashi.

Sauran sun Aminu Danjibga, Maniru Gidanjaja, Yusuf Moriki, and Kabiru Moyi.

NAN ta kuma ruwaito cewa jam'iyyar APC ne ta lashe dukkan kujerun majalisar dokoki na jiha 24 a zaben gudanar a ranar Asabar 9 ga watan Maris.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel