Mijina ya kashe diyarmu don yin tsafin samun kudi – Uwargida ga Kotu

Mijina ya kashe diyarmu don yin tsafin samun kudi – Uwargida ga Kotu

Wata Mata mai suna Rafiat Okunola ta shaida ma wata kotun gargajiya dake zamanta a Ile-Tuntun cikin garin Ibadan na jahar Oyo yadda mijinta, wanda basa tare a yanzu, Kasali Adeleke yayi amfani da diyarsu don samun arzikin duniya ta hanyar kasheta.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito uwargida Rafiat ta bayyana haka ne a zaman kotun na ranar Laraba, 13 ga watan Maris, dayake dama tun a shekarar 2016 shugaban kotun, Cif Henry Agbaje ya kashe auren ma’auratan akan Adeleke na dukanta.

KU KARANTA: CUPP ta zargi Buhari da hannu cikin zaben Alkalai 5 da zasu saurari shari’arsa da Atiku

Baya gar aba aurensu a wancan lokaci, kotun ta mika ma Adeleke mallakin yayansu guda uku tunda sun manyanta a lokacin, sa’annan ta shawarci Rafiat akan ta garzayo gaban kotun a duk lokacin da take bukatar ganin yayan nata.

Sai dai a zaman kotun na Laraba, Rafiat ta roki kotu data dawo mata da mallakin sauran yayansu biyu da suka rage a hannun ubansu, gudun kada ya salwantar da rayuwarsu kamar yadda ya kashe guda daya daga cikinsu don yin tsafin kudi.

“Na shiga rudani matuka a lokacin da babban diyata ta shaida min cewa kanwarsu ta mutu, kuma mahaifinsu Adeleke ya binneta shi kadai, sai na tambayi yan uwana dake mazauna garin Ibadan don yin sanadiyyar mutuwar yarinyar, amma babu wanda yasan lokacin da ta mutu, don haka nake tunanin tsafi yayi da ita.” Inji ta.

Sai dai Adeleke ya musanta zargin, inda yace a gaban mahaifiyar Adeleke, kannenta mata guda uku da kuma wani surukinsu na binne diyar tasu da ta rasu, don haka ba wani boyayyen lamari bane.

Shima Adeleke ya zargi Rafiat da safarar kananan yara, inda ya shaida ma kotu cewa sakamakon diyarsu data rasu tana dauke da lalurar ciwon kafa, Rafiat tayi ta kokarin ganin ta sayar da ita ga masu cinikin yara don ta rabu da ita ta huta.

Sai dai bayan sauraron dukkanin bangarorin a wannan shari’a mai sarkakiya, Alkalin kotun ya dage sauraron karar zuwa ranar 4 ga watan Afrilu, sa’annan ya umarci Adeleke da Rafiat dasu kawo kwararan hujjoji game da zarge zargen da suke yi ma juna, kuma kowannensu ya taho da yan uwansa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng