Lokuta 3 da aka Kai wa Donald Trump Hari da Bindiga za a Kashe Shi a Tarihi
Shugaban Amurka, Donald Trump ya fuskanci hare-hare da bindiga a lokuta mabanbanta, inda da aka nemi kawo karshen rayuwarsa.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
America - A makon da ya wuce wani matashi dan kasar Amurka ya je wajen da ake taron da Donald Trump ya halarta, ya fara harbi da bindiga.
Hukumomin kasar Amurka sun tabbatar da cewa sun kama matashin mai suna Cole Tomas Allen da ya yi harbin kuma ana zarginsa da yunkurin kashe Trump.

Source: Getty Images
A wannan rahoton, mun kawo muku bayanai game da wasu lokuta uku da aka taba yunkurin kashe shugaban Amurka, Donald Trump.
1. An harbi Donald Trump a Pennsylvania
Al Jazeera ta rahoto cewa Shugaban Amurka ya samu rauni a wani harin bindiga yayin wani gangamin yaƙin neman zaɓe a Butler County a ranar 14 ga Yuli, 2024, watanni uku kafin a sake zaɓensa a karo na biyu.

Kara karanta wannan
Amurka ta tafka asara a yaki da kasar Musulunci ta Iran, ta kashe kimanin Dala biliyan 25
Yayin da Trump ke jawabi ga jama’a, an ji aƙalla harbe-harbe biyar da misalin ƙarfe 6:15 na yamma. Nan take ya sunkuya, yayin da jami’an tsaron Amurka da dama suka ruga kan dandalin domin kare shi.
Bayan ‘yan mintuna, jami’an suka taimaka masa ya tashi tsaye sannan suka raka shi zuwa cikin ayarin motocinsa, inda aka ga jini a kunnen damansa yana kuma zuba a fuskarsa.

Source: Getty Images
Jami’an tsaron sun harbe tare da kashe wanda ake zargi cikin daƙiƙu bayan fara harbin. Kafin a dauke shi, an ga Trump yana daga hannuwansa yana ihu ga jama’a.
Daga baya, hukumar FBI ta bayyana sunan wanda ya kai harin a matsayin Thomas Matthew Crooks mai shekaru 20 daga Bethel Park, Pennsylvania.
2. An so kashe Trump a Florida
A ranar 15 ga Satumba 2025, an yi yunkurin kashe Trump yana a wurin shakatawansa na West Palm Springs a Florida da misalin ƙarfe 2:00 na rana.
Rahotannin kafafen yada labarai na yankin sun ce Trump yana motsawa tsakanin rami na biyar da na shida a filin wasan golf tare da abokinsa, Steve Witkoff lokacin da aka ji karar harbe-harbe.
Jami’ai sun ce wani jami’in tsaro ya hango bakin bindiga a cikin wani waje mai ciyawa kusa da gefen filin. Jami’ai da dama sun harba aƙalla harsasai hudu a wajen.
Bayan dogon bincike da hukumomi suka yi, sun bayyana wanda ake zargin a matsayin Ryan Wesley Routh mai shekaru 58.

Source: Getty Images
Masu gabatar da kara sun ce Routh ya zauna a Kudancin Florida na kusan wata guda, kuma bayanan wayarsa sun nuna yana kusa da gidan Trump na Mar-a-Lago.
Ma'aikatar shari'a ta kasar Amurka ta sanar da cewa a watan Fabrairun 2026 aka yanke masa hukuncin daurin rai da rai bayan an same shi da laifin shirya kashe Trump.
3. Yunkurin kashe shugaban kasa a White House
A ranar 25 ga watan Afrilun 2026 Fox New ta rahoto an kama wani matashi mai suna Cole Tomas Allen mai shekaru 31 bayan bude wuta a kusa da wajen da Trump ya ke.
An gurfanar da matashin dan asalin California da ake tuhuma da kokarin kashe Shugaba Trump, kuma masana masu nazarin tsattsauran ra’ayi na bibiyar shari'ar.

Source: Getty Images
Ana zargin Allen, malami a makarantar sakandare wanda ya yi karatu a fannin kimiyyar kwamfuta, da mallakar manyan makamai ba bisa ka'ida ba.
Makaman da Allen ya mallaka
A wani labarin, mun kawo muku cewa hukumomin Amurka sun gurfanar da wani matashi, Cole Tomas Allen bisa zargin yukurin kashe Donald Trump da wasu tuhume-tuhume.
Yayin zaman kotu, hukumomi sun fitar da hotunan makaman da aka samu Cole Tomas Allen da su da suka hada da bindigogi guda biyu.
Haka zalika an gabatar da wasu wukake guda uku da aka ce matashin ya so ya yi afani da su wajen kai hari kai tsaye kan shugaban kasar Amurka.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

