Zabe: Yadda ‘yan ta-more suka kasha ‘yan sanda biyu a Sokoto – Kwamishina

Zabe: Yadda ‘yan ta-more suka kasha ‘yan sanda biyu a Sokoto – Kwamishina

- Kwamishinan ‘yan sandan jihar Sokoto, Aminu Koji, ya bayyana cewar wasu ‘yan bindiga ne su ka kaddamar da harin kwanton bauna a kan jami’an ‘yan sanda

- Koji ya kara da cewa, ‘yan bindigar sun kasha jami’an ‘yan sanda biyu a harin da ‘yan bindigar su ka kai ranar juma’a, 8 ga watan Maris

- An kaiwa jami’an ‘yan sandan hari ne yayin da su ke kan hanyar su ta zuwa aikin zabe a karamar hukumar Isa

Kwamishinan rundunar ‘yan sanda a jihar Sokoto, Aminu Koji, ya ce wasu jami’an ‘yan sanda biyu sun rasa ran su sakamakon harin kwanton bauna da ‘yan bindiga su ka kai ma su a hanyar su ta zuwa aikin zabe a karamar hukumar Isa.

A ranar Juma’a, 8 ga watan Maris, ne wasu ‘yan bindiga su ka kai hari a kan jami’an ‘yan sanda a jihar Sokoto, kamar yadda rahotanni su ka bayyana.

Koji ya mika sakon ta’aziyya ga iyalan jami’an ‘yan sandan da aka kasha da aka kashe yayin da su ke kan aikin yiwa kasa hidima.

Da ya ke ganawa da manema labarai a yau Laraba, 13 ga watan Maris, Koji ya bayyana sunayen jami’an biyu da aka kashe; Asp Abdullahi Maisaje da saja Usman Ibrahim.

Zabe: Yadda ‘yan ta-more suka kasha ‘yan sanda biyu a Sokoto – Kwamishina
Aminu Waziri Tambuwal
Asali: UGC

Ya bukaci iyalan mamatan da su kasance ma su juriya da rungumar kaddarar da Allah ya dora ma su, sannan ya kara da cewa; “Allah ne mai kashe wa da raya wa.”

Kwamishinan ya sanar da cewar gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, ya bawa iyalan mamatan biyu gudunmawar Naira miliyan biyu, kowa miliyan guda.

DUBA WANNAN: Sojoji sun kashe ‘yan bindiga 55, sun kubutar da mutane 760 a Zamfara

Koji ya yi godiya ga Tambuwal a kan tausayin da ya nuna a kan iyalan mamatan. Ya kara da cewar kudin da gwamnan ya bayar ba fansar ran jami’an ba ne, tallafi ne kawai ga iyalan su. Kwamishinan ya danka kudaden ga matan ‘yan sandan biyu da aka kasha.

Maryam Abubakar, matar marigayi Maisaje, ta godewa gwamnan bisa tausayar da ya nunua gare su. Ta bayyana cewar marigayin yam utu ya bar ta da ‘ya’ya 9; maza hudu, mata biyar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng