Za ayi bala'i idan ku ka yi yunkurin magudi a zabukan da za a maimaita - Gargadin 'yan majalisa ga INEC da APC

Za ayi bala'i idan ku ka yi yunkurin magudi a zabukan da za a maimaita - Gargadin 'yan majalisa ga INEC da APC

Wasu 'yan majalisar wakilai na tarayya sun gargadi jam'iyyar All Progressives Congress (APC) da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta INEC da su guji aikata duk wani magudi a zabukan da za a maimaita bayan soke su da akayi a wasu jihohi.

Da suke tsokaci a kan yadda Hukumar Zaben ta soke zabuka da dama a wasu johohin Najeriya, 'yan majalisar sunyi gargadin cewa muddin ba a gudanar da sahihiyar zabe ba kasar za ta fada cikin tashin hankali.

A yayin da ya ke gabatar da kudirin a gaban majalisa, Sunday Karimi na jam'iyyar PDP daga jihar Kogi ya ce ayyana cewa zabe bai kammalu ba a yayin da ake kirga kuri'u ya sabawa doka kuma dabara ce da INEC keyi domin sauya abinda al'umma suka zaba.

DUBA WANNAN: APC 13, PDP 9: Jerin sunayen sabbin gwamnoni da INEC ta sanar sun lashe zabe

Najeriya za ta kama da wuta idan APC da INEC su kayi magudi a zabe zagaye na biyu - Dan Majalisa
Najeriya za ta kama da wuta idan APC da INEC su kayi magudi a zabe zagaye na biyu - Dan Majalisa
Asali: Twitter

Hakan yasa ya yi kira ga majalisar ta sake duba dokar zabe na kasa domin yi masa garambawul ta yadda hakan ba zai sake faruwa a gaba ba.

"Ina tunanin ya dace a sake bibiyar Dokar Zabe domin magance matsalar rashin kammala zabe da ya zama abin kunya ga demokradiyar mu.

"Ya zama dole muyi gyara a kan dokar domin dokar tana gaba da duk wani umurni na Hukumar INEC," a cewar Karimi.

Ali Madaki na jam'iyyar PDP daga jihar Kano ya ce sanar da cewa zaben Kano bai kammalu ba zai iya jefa jihar cikin tashin hankali, "musamman duba da cewa APC tana shirin amfani da dukkan karfin ikon da ke hannunta domin kwashewa al'umma abinda suka zaba.

"Ina son in sanar da su cewa Kano daban ce. Kano ba Legas ba ce kuma al'ummar Kano ba za su amince da magudin zabe ba. Dole mu taka musu birki idan kuma suka dage sai sunyi hakan toh Najeriya za ta kama da wuta," Madaki ya yi gargadi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel