Akuya za ta jagoranci ragamar mutanen Vermont a Amurka
Wani abin mamaki ya faru a Duniya a cikin makon nan, inda aka samu wasu Mutane a can kasar Amurka watau USA da su fito, su ka zabi wata akuya a matsayin shugabar su. Jaridun kasashen waje su ka bada wannan labari.
Mutanen wani karamin kauye mai suna Vermont da ke cikin Amurka, sun zabi wata Akuya ne a matsayin wanda za ta jagorance su. Sunan wannan Akuya Lincoln. Ana sa rai wannan zabe da aka yi ya zama wani darasi a siyasa.
Ko da dai dabba ce, amma wasu su na ganin akwai baiwa na musamman da Ubangiji ya ba wannan Akuya don haka aka zabe ta da shugabanci a karkarar na Vermont. Wannan Akuya mai shekaru 3 da haihuwa tana da manyan kunnuwa.
KU KARANTA: Bayan yayi aikin tukin motar haya na shekaru 16, Zulum ya zama Gwamna
Lincoln tayi takara ne a Ranar Talata inda ta doke sauran masu neman wannan kujera na Mai Gari (Watan Mayor na Garin Fair Haven da ke cikin Vermont) irin su Crystal the gerbil da kuma wasu tarin dabobbi na kyanwa da karnunaka.
Akwai mutane akalla 2500 a wannan kauye na Fair Haven don haka ake sa rai wannan kare ya tabuka wani abu. Kawo yanzu dai a wannan gari babu Kantoma (Mayor), sai dai wanda ke rike da mukamin Sarkin Unguwa (Town Manager).
Joseph Gunter, wanda ke rike da wannan kujera a Fair Haven shi ne ke yin duk wasu aikce-aikace da ya kamata wannan Akuya tayi a yanzu. A zaben da aka yi, Akuyar ta samu kuri’a 13 ne inda ake sa ran cewa zaben badi zai fi kyau.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa
Ko a http://twitter.com/legitnghausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT
mal
Asali: Legit.ng