A Karshe, Gwamnan Bauchi zai Sauya Sheka, Ya Fadi Kujerar da zai Nema a 2027
- Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed, ya ce zai fita daga jam'iyyar adawa ta PDP sakamakon hukuncin Kotun Daukaka Kara
- Ya bayyana cewa zai koma zuwa wata jam’iyya ta dabam nan ba da jimawa ba, domin a cewarsa lokaci na neman kurewa 'yan adawa
- Bala Mohammed ya kuma sanar da kujerar da zai nema a zaben 2027 a lokacin da aka yi masa tambaya a kan ko zai nemi shugaban kasa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Bauchi - Gwamnan Bala Mohammed na jihar Bauchi ya sanar da cewa nan da kwanaki masu zuwa za a ji labarin inda ya dosa a siyasa.
Hakan na zuwa ne bayan hukuncin da kotun daukaka kara ta yi na rusa taron da jam'iyyar PDP ta yi a birnin Ibadan na jihar Oyo.

Source: Facebook
A wani bidiyo da tashar BBC Hausa ta wallafa a shafinta na X, Bala Mohammed ya bayyana kujerar da zai nema a zaben 2027.
Maganar Bala Mohammed kan hukuncin kotu
Bala Mohammed ya bayyana cewa sun karbi hukuncin da kotu ta yi game da karar da aka shigar da su domin ba ya nuna cewa sun fadi warwas.
Ya ce duk da kotu ta rusa taron da suka yi a Ibadan, kotun ta kuma rusa shugabannin PDP da bangaren Nyesom Wike ya kafa.
Gwamnan ya bayyana cewa Wike da 'yan bangaren shi aiki suke yi wa APC, ya tsaya ne a jam'iyyar PDP ne domin ya kawo masu cikas.
Gwamna Bala zai sauya sheka daga PDP
Bala Mohammed ya ce ya riga ya tattauna da mutanensa a Bauchi domin sauya sheka da za ta ba su damar yin takara a zaben 2027.
Gwamnan ya ce za su nemi jam'iyya mai tsafta da ba ta da rigingimu domin su shiga su yi takara, kuma nan gaba kadan za a ji ina suka dosa.

Source: Facebook
Ya kara da cewa manyan PDP kamar Tanimu Turaki da sauransu za su tsaya a jam'iyyar su kwato hakkinsu yayin da su kuma za su sauya sheka.
Bala Mohammed zai yi takara a 2027
Sanata Bala Mohammed ya bayyana cewa ba zai yi takarar shugaban kasa ba a 2027, domin a PDP ma sun mayar da batun tsayawa takara zuwa Kudu.
Ya bayyana cewa zai nemi takarar Sanata a Bauchi ta Kudu domin cigaba da kawo ayyukan alheri ga mutanen da zai wakilta.
Ya ce:
"Yanzu abin da na ke so na tsaya bisa kiranye-kiyanye da na samu shi ne in tsaya Sanata a Bauchi ta Kudu in samu dama in cigaba da ba da jagoranci da kuma wakilici wa mutane."
A kan batun dunkulewar 'yan adawa kuma, ya ce suna tattaunawa da su Rabiu Kwankwaso, Peter Obi da sauransu amma matsalolin da suke fuskanta sun bambanta.
Batun sauya shekar Kwankwaso/Obi
A wani labarin, kun ji cewa ana cigaba da rade-radin cewa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da Peter Obi za su fice daga jam'iyyar ADC.
Hakan na zuwa ne yayin da jam'iyyar ke cigaba da fuskantar rikicin cikin gida da kuma shari'a a kotu duk da zabe na kara karatowa.
Masana sun yi gargadin cewa sauya shekar za ta iya haifar da matsala musamman lura da yadda 'yan adawa ke burin kifar da Bola Tinubu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


