Da Gaske An Haramta Wa Jam'iyyar ADC Tsayar da 'Yan Takara a Zaben 2027? An Samu Bayani

Da Gaske An Haramta Wa Jam'iyyar ADC Tsayar da 'Yan Takara a Zaben 2027? An Samu Bayani

  • Jam'iyyar ADC ta musanta rahotannin da ake yadawa cewa ba za ta samu damar tsayar da 'yan takara ba a babban zaben 2027
  • Mai magana da yawun ADC na kasa, Bolaji Abdullahi ya ce wadannan labarai ba su da tushe, an kirkire su ne domin haifar da rudani
  • Jam’iyyar ta kara da cewa tana ci gaba da gina kanta a matsayin babbar jam’iyyar adawa, tare da mai da hankali kan tattara goyon bayan ‘yan Najeriya

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria – Jam’iyyar hadaka ta ADC ta bayyana cewa za ta tsayar da ‘yan takara a babban zaben 2027, tana mai watsi da rahotannin da ke cewa ba za ta shiga zaben ba.

ADC ta bayyana rahotannin da ake yadawa cewa ba za ta samu damar shiga zaben 2027 a matsayin marasa tushe, inda ta yi ikirarin shiga a dama da ita kamar yadda doka ta tanada.

Kara karanta wannan

Ganduje, manyan APC sun saya wa Abba fam, an tara N50bn don takarar Tinubu a 2027

Bolaji Abdullahi.
Mai magana da yawun jam'iyyar adawa, ADC, Bolaji Abdullahi Hoto: Bolaji Abdullahi
Source: Facebook

Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da sakataren yada labarai na jam’iyyar ADC na kasa, Mallam Bolaji Abdullahi, ya fitar a ranar Asabar, kamar yadda Leadership ta ruwaito.

ADC ta jaddada kudirin ceto Najeriya

Jam’iyya ADC ta ce duk da wasu abubuwan da ta kira “tashin hankali da suka faru a baya-bayan nan,” tana ci gaba da mai da hankali kan burinta na ceto Najeriya daga abin da ta kira gazawar gwamnatin APC.

Sanarwar ta ce:

“Jam’iyyar ADC na son bayyana karara cewa muna nan kan kudurinmu na ceto Najeriya daga gazawar gwamnatin APC da kuma dakile barazanar komawa tsarin jam’iyya daya.”

Ta kara da cewa zargin cewa jam’iyyar ba za ta tsayar da ‘yan takara ba a zaben 2027 “ba shi da tushe kuma an kirkiro shi ne domin haifar da rudani.”

ADC za ta samu shiga zaben 2027?

Jam’iyyar ta jaddada cewa babu wata matsala ta doka da za ta hana ta shiga zaben, tana mai cewa tana bin kundin tsarin mulki da dokar zabe yadda ya kamata.

Kara karanta wannan

Martanin Nafi'u Bala ga hukuncin kotun koli game da shari'ar rikicin ADC

“Ya kamata kowa ya san cewa ADC za ta tsayar da ‘yan takara a zaben 2027, ‘yan takara masu kwarewa, nagarta da karbuwa a fadin kasa,” in ji sanarwar.

Jam’iyyar ta kara da cewa tana ci gaba da gina kanta a matsayin babbar jam’iyyar adawa, tare da mai da hankali kan tattara goyon bayan ‘yan Najeriya da kuma gina tsari mai karfi domin lashe zabe.

ADC .
Tambarin jam'iyyar hadakar yan adawa ta ADC Hoto: ADP Party
Source: Twitter

Abubuwan da ADC ta maida hankali

Ta kara da cewa:

“Ba mu damu da hayaniya ba. Mun mayar da hankali kan aikin da ya dace, samun goyon bayan jama’a, hada kan ‘yan Najeriya da suka gaji da rashin tsaro, tsadar rayuwa da karancin damammaki.”

ADC ta bukaci mambobinta da magoya bayanta da su yi watsi da irin wadannan rahotanni, tana mai cewa abin da ke gaba na bukatar hadin kai da jajircewa, ba rade-radi ba.

Rigima ta kunno kai kan takara a ADC

A wani rahoton, kun ji cewa jam’iyyar ADC na fuskantar rikici kan wanda zai tsaya takarar shugaban kasa a zaɓen shekarar 2027 da ake tunkara.

Har yanzu ADC na fama da shari’o’i daban-daban a kotu, yayin da wasu tsofaffin mambobi ke nuna bacin rai kan yadda sababbin shiga suka mamaye jam’iyyar.

Rigima ta kara kunno kai a ADC ne game da takara tsakanin Peter Obi, Atiku Abubakar, Rabiu Kwankwaso da Rotimi Amaechi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262