Babbar Magana: Faransa Ta Ja Kunnen Isra'ila kan kai wa Kiristoci Hari
- Faransa ta yi Allah-wadai da karuwar hare-haren da ake yi wa Kiristoci da aka ce gwamnatin Isra'ila karkashin Netanyahu ne ke kai wa
- Rahotanni sun nuna cewa Ministan harkokin wajen Faransa, Jean-Noel Barrot ne ya yi magana bayan wani mummunan hari da aka kai
- Hakan na zuwa ne yayin da Isra'ila ke kai hare-hare Lebanon, inda kungiyar Hezbollah ke mayar da martani duk da cewa an tsagaita wuta
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Faransa - Ministan harkokin wajen Faransa, Jean-Noel Barrot, ya ce kasarsa ba za ta lamunci karuwar hare-haren da ake yi wa Kiristoci a Jerussalam ba.
Barrot ya yi nuni da wani mummunan hari da aka kai wa wata malaman cocin Katolika ‘yar Faransa a Yammacin Kudus, wanda ya janyo bacin rai sosai a wannan makon.

Source: Getty Images
Legit ta tattaro bayanai game da abubuwan da Jean-Noel Barrot ya fada ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Asabar.
Zargin da Faransa ta yi wa Isra'ila
A ranar Alhamis da ta wuce, ‘yan sandan Isra’ila sun fitar da bidiyo da ke nuna harin da aka kai wa wata malamar cocin Katolika a Kudus.
Hotunan sun nuna wani mutum yana bin malamar cocin, ya ture ta da karfi har ta fadi kasa, lamarin da ya jikkata ta, sannan ya dan tafi kafin ya dawo ya sake bugunta tana kwance a kasa.
Barrot ya ce Faransa ta nuna matukar damuwa tare da fatan matar za ta murmure cikin gaggawa.
Al Jazeera ta rahoto ya ce:
“Bayan wannan hari mai tayar da hankali da ‘yar kasarmu ta fuskanta a Kudus, na bayyana mata matukar damuwata, goyon baya na, da kuma fatan ta warke cikin gaggawa.
"An kama wanda ya aikata wannan mummunan aiki.
"Dole ne a masa hukuncin da wasu za su dauki darasi daga gare shi domin dakatar da hare-haren da ake yi wa Kiristoci a Kasa Mai Tsarki, hare-haren da Faransa da ke da alhakin kare al’ummomin Katolika da wuraren ibada ba za ta lamunta ba.”

Source: Getty Images
Hezbollah ta kai hari kan Isra’ila
Yayin da ake cigaba da kai hare-hare, kungiyar Hezbollah ta ce ta kai hari kan taron sojojin Isra’ila a cikin wani gida a garin Biyyada da ke Kudancin Lebanon.
Kungiyar ta ce ta kai harin ne da misalin karfe 7:15 na yamma a ranar Juma’a. Ba a san adadin sojojin da ke cikin gidan ba, ko sakamakon harin, ko kuma ko akwai wadanda suka jikkata ko suka mutu.
Isra’ila ta kaddamar da yaki a Lebanon tun daga ranar 2 ga Maris 2026, inda aka kashe sama da mutane 2,600 tare da raba fiye da miliyan 1.6 da muhallansu.
Ana son kifar da Netanyahu a zabe
A wani labarin, mun kawo muku cewa manyan 'yan adawa a kasar Isra'ila sun ce za su hada kai domin yakar gwamnatin Benjamin Netanyahu a zabe mai zuwa.
Shugabannin 'yan adawa sun ce Benjamin Netanyau bai kawo wani cigaba ba a kasar duk da shekarun da ya shafe a matsayin Firaminista.
Bincike ya nuna cewa 'yan adawar da suke son haduwa sun taba hada kai a bayan sun kayar da Benjamin Netanyahu da wasu mutanensa.
Asali: Legit.ng


