Kwankwaso Ya Yi Karin Haske kan Jita Jitar Koma wa NDC da Obi domin Yin Takara

Kwankwaso Ya Yi Karin Haske kan Jita Jitar Koma wa NDC da Obi domin Yin Takara

  • Tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi martani game da yada wasu rahotanni da ake yi kan makomar siyasarsa
  • Jagoran darikar Kwankwasiyya ya ce ya yi karin haske kan rahotannin haɗakarsa da Peter Obi gabanin zaɓen shugaban ƙasa na 2027
  • Kwankwaso ya bayyana cewa har yanzu babu wata matsaya kan takarar shugaban ƙasa ko wanda zai zama mataimakin ɗan takara

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kano - Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso ya yi martani kan wasu rahotanni da ke cewa zai koma NDC.

An yi ta yada rahotannin cewa ya shirya barin ADC da shi da tsohon gwamnan Anambra, Peter Obi domin yin takara a 2027.

Kwankwaso ya yi martani kan labarin shirin barin ADC
Sanata Rabiu Kwankwaso suna gaisawa da Peter Obi a taron siyasa. Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso.
Source: Twitter

Kwankwaso ya bayyana haka ne a shafinsa na X inda ya ƙaryata rahotannin da ke cewa ya yanke shawarar tsayawa takarar shugaban ƙasa a 2027.

Kara karanta wannan

Sanatan APC ya bijirewa gwamna, ya yi fatali da zabin wanda zai gaje shi a 2027

Kwankwaso ya yi karin haske kan makomar siyasarsa

Kwankwaso ya kuma bayyana cewa bai amince da wani ɗan takara a matsayin abokin takararsa ba, duk da rade-radin haɗakarsa da Peter Obi.

Rahotanni sun nuna cewa ana ta yaɗa fastocin haɗin gwiwar Kwankwaso da Obi a kafafen sada zumunta tun bayan taron jam’iyyun adawa da aka yi a Ibadan.

An kuma yi zargin cewa su biyun na shirin ficewa daga ADC zuwa wata jam’iyya mai suna jam'iyyar NDC saboda rikicin cikin gida da ke addabar ADC.

Sai dai Kwankwaso ya ce babu wata matsaya ta ƙarshe da aka cimma kan makomarsa ta siyasa ko ta magoya bayansa zuwa yanzu.

Ya bayyana cewa ADC ma ba ta kai ga yanke hukunci kan wanda zai samu tikitin shugaban ƙasa ko yadda za a raba mukamai ba.

Kwankwaso ya tabo batun takarar a zaben 2027
Sanata Rabiu Kwankwaso yayin ganawa da manema labarai. Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso.
Source: Facebook

Kwankwaso ya karyata batun takarar shugaban kasa

Kwankwaso ya ce duk rahotannin da ke cewa ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takara ko goyon bayan wani ɗan takara ba su da tushe.

Kara karanta wannan

Zargin kisan Kiristoci: Amurka za ta dauki mummunan mataki kan kasar Najeriya

Dan siyasar ya danganta halin da ADC ke ciki da hukuncin kotun koli da ya soke umarnin kotun ɗaukaka ƙara kan rikicin shugabancin jam’iyyar.

Ya ce rikicin ya jefa ADC cikin mawuyacin hali, lamarin da ya sa suka fara tattaunawa da shugabannin NDC da PRP kan matakin gaba.

Kwankwaso ya ƙara da cewa rashin halartarsa wasu tarukan ADC ba yana nufin zai sauya jam’iyya ba, domin yana da wasu uzurori na kashin kansa.

Jita-jitar da aka fara yadawa ta jawo maganganu da kuma saka shakku a zukatan wasu yan Najeriya musamman game da cewa wai Kwankwaso zai sake barin ADC zuwa NDC.

Kwankwasiyya na duba yiwuwar hadaka da NDC

An ji cewa kungiyar Kwankwasiyya ta bayyana yadda ta ke kallon hukuncin kotun kolin Najeriya a kan rikicin shugabancin jam'iyyar ADC.

Kwanaki biyu bayan hukuncin, Kwankwasiyya ta bayyana cewa tana nazari tare da duba yiwuwar sabuwar haɗakar siyasa.

Ƙungiyar ta ce hukuncin ya ƙara masu kwarin gwiwa kan adalci a tsarin shari’ar kasar nan, amma duk da haka tana duba batun.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.