Hotuna da bidiyon yadda ake ceto daliban makarantar da ta rubza a Legas
Al'ummar jihar Legas sun waye gari cikin wata annoba na rubzawar makaranta darajar farko wato Nozare da firamare a karamar hukumar Lagos Island dake jihar.
Ginin makarantar mai hawa ukku da ke yankin Itafaji, tsibirin Legas ya rubza a ranar Laraba, 13 ga watan Maris, 2019. Lamarin da ya haddasa tashin hankali da rudani tsakanin al'ummar da ke zaune a kusa da ginin.
Zuwa yanzu, ana cigaba da kokarin ganin an fitar da dukkan yaran da ginin ya rubza da su kuma an samu ceto kimanin mutane 41 amma kash! an tabbatar da mutuwa 12.
Akalla dalibai da malaman makaranta 71 ke cikin ginin yayinda ta rubzo.
Kalli abinda ke faruwa cikin hotuna:
KU KARANTA: Jerin sunayen yara 41 da aka ceto a rubzawar ginin makaranta a Legas
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng