Jami’an hukumar kwastam sun yi wani babban kamu a jahar Borno

Jami’an hukumar kwastam sun yi wani babban kamu a jahar Borno

Jami’an hukumar kwastam reshen jahar Borno-Yobe sun kama wata katuwar Motar tirela makare da shinkafar kasar waje buhuna dari uku da aka yi safararsu ta jahar Borno, kamar yadda hukumar ta sanar a ranar Laraba, 13 ga watan Maris.

Kwamandan yankin, Abdullahi Biu ne ya sanar da haka a garin Maiduguri yayin da yake ganawa da manema labaru, inda yace sun kama Motar ne akan hanyar Bama zuwa Banki a ranar 5 ga watan Maris.

KU KARANTA: Sunayen mutanen da zasu tsara shagulgulan da za’ayi a bikin rantsar da shugaban kasa Buhari

Jami’an hukumar kwastam sun yi wani babban kamu a jahar Borno
Shinkafar
Asali: UGC

Kwamanda Biu yace sun samu labarin motar tana dauke da shinkafa ne, amma an lullube buhunan shinkafar da gawayi da abincin dabbobi, haka zalika yace sun samu nasarar cafke direban motar yayin da yayi kokarin tserewa.

A cewar kwamandan, baya ga shinkafa da motar take dauke dasu, akwai kuma busashshen kifi, sabulai, masara, alkama da kuma waken suya, duka a cikin wannan motar, inda aka yi amfai dasu wajen boye shinkafar.

Game da yanayin samun kudaden shiga a yankin kuwa, Kwamandan yace “A shekarar 2018 mun tara naira miliyan 136, duk da matsalar Boko Haram, hakanan mun kama motoci guda tara, wadanda aka biya musu kudin fito daya kai naira miliyan 283” Inji shi.

Daga karshe Kwamandan ya koka game da ayyukan yayan kungiyar ta’addanci na Boko Haram game da raguwar kudaden shiga da suke samu a yankin, sa’annan ya danganta raguwar kudaden shigar ga haramta shigo da busashshsen kifi da hukumar ta yi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel