Dalilin da Ya Sa Kwankwaso da Peter Obi Ke Shirin Barin ADC

Dalilin da Ya Sa Kwankwaso da Peter Obi Ke Shirin Barin ADC

  • Alamu sun nuna jam'iyyar ADC na shirin rasa tsofaffin 'yan takarar shugaban kasa a zaben 2023, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da Peter Obi
  • Manyan 'yan siyasar dai na duba yiwuwar ficewa daga jam'iyyar ADC wadda take son kawar da APC a zaben 2027
  • Majiyoyi sun bayyana cewa dalilinsu na ficewa daga ADC na da nasaba da wasu abubuwan da ke faruwa a cikinta

​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Alamu sun nuna Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da Peter Obi na shirin ficewa daga jam'iyyar ADC zuwa NDC.

Ficewar Kwankwaso da Peter Obi za ta kawo cikas ga shirye-shiryen shugabannin jam’iyyun adawa na tsayar da ɗan takara guda ɗaya a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

Peter Obi da Kwankwaso na shirin barin ADC
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso tare da Peter Obi Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso
Source: Facebook

Majiyoyi a cikin hadaka sun shaida wa jaridar The Punch dalilin da ya sa manyan 'yan siyasar ke shirin ficewa ADC.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya yi karin haske kan jita jitar koma wa NDC da Obi domin yin takara

Meyasa Obi da Kwankwaso za su bar ADC?

Sun bayyana cewa shirin ficewar Obi da Kwankwaso ya samo asali ne sakamakon fargabar da take ƙaruwa kan yadda tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar yake da tasiri a cikin ADC, wadda ake tunanin za a yi amfani da ita a matsayin babban dandamalin ƙawancen.

An yi amanna cewa Atiku yana da kyakkyawar dama ta samun takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar gabanin Obi da tsohon Ministan sufuri, Rotimi Amaechi.

Shirin ficewar Obi da Kwankwaso yana zuwa ne ƙasa da mako guda bayan shugabannin jam’iyyun adawa sun amince su yi aiki tare don tsayar da ɗan takara guda ɗaya domin kawar da jam’iyya mai mulki ta APC a 2027.

An cimma wannan yarjejeniya ne a babban taron shugabannin jam’iyyun adawa na ƙasa da aka gudanar a Ibadan, jihar Oyo.

Wannan yarjejeniya tana ɗaya daga cikin ƙuduri tara da ke cikin sanarwar bayan taro wadda shugabannin adawar suka karanta a ƙarshen taron.

Kara karanta wannan

Zance ya kare: Kwankwaso ya gama yanke shawara, zai bar ADC tare da Peter Obi

Kwankwaso da Obi za su koma wata jam'iyya

Jaridar TheCable ta ce sakataren kwamitin amintattu na jam’iyyar NNPP Buba Galadima, ya bayyana cewa Obi da Kwankwaso, tare da sauran manyan mambobin ƙawancen adawa, za su sanar da sabon dandamalin siyasa a ranar Litinin, 4 ga watan Mayun 2026.

Kodayake bai ambaci sunan dandamalin ba, majiyoyi na kusa da tsofaffin gwamnonin sun bayyana cewa shugabannin biyu suna kammala shirye-shiryen shiga jam’iyyar NDC, wadda tsohon gwamnan jihar Bayelsa, Sanata Seriake Dickson, ke jagoranta.

Kwankwaso da Peter Obi na duba yiwuwar barin ADC
Tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso
Source: Facebook

Akwai rarrabuwar kai tsakanin 'yan adawa

Wani mai sharhi kan al’amuran siyasa, Adebayo Abubakar, ya yi gargaɗin cewa rarrabuwar kai, rashin amincewa da juna, da kuma son zuciya na kashin kai a tsakanin shugabannin adawa na iya bai wa Shugaba Bola Tinubu hanyar da ta fi sauƙi na sake cin zaɓe a 2027.

Adebayo Abubakar ya ce sauye-sauyen siyasa da suka shafi manyan jiga-jigan adawa kamar Obi da Kwankwaso sun nuna cewa har yanzu jam’iyyun adawar suna da sauran rina a kaba wajen nuna haɗin kai da zai iya ƙalubalantar jam’iyya mai mulki ta APC.

Kara karanta wannan

2027: Rigima ta kunno kai a ADC kan 'tikitin' Kwankwaso/Obi da Atiku, Amaechi

“Idan ka kalli abin da ke faruwa a sansanin adawa, abu na farko da yake bayyane shi ne matsalar rashin amincewa da juna da kuma rashin son manyan jaruman su sadaukar da burinsu na kashin kai domin cimma burin bai-ɗaya na kawar da jam’iyya mai mulki."

- Adebayo Abubakar

Jigo a Kwankwasiyya ya bar ADC

A wani labarin kuma, kun ji cewa wani jigo a tafiyar Kwankwasiyya daga jihar Kano, Hon. Adamu Abdullahi, ya sanar da ficewarsa daga jam'iyyar ADC.

Hon Adamu Abdullahi a cikin wasikar da ya fitar, ya bayyana cewa ya fice daga jam’iyyar hamayya ta ADC nan take ba tare da ɓata lokaci ba.

Tsohon mamban na ADC yana daga cikin fitattu kuma jiga-jigan Kwankwasiyya a Dala, kuma yana cikin masu neman takarar kujerar majalisar dokokin jihar Kano.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng