Latest
Mun ji cewa an kashe wasu ‘Yan bindiga a bakin fadar Sarkin Birnin Magaji a Jihar Zamfara. Jama’a sun shiga har fadar Sarkin Garin ne inda su ka kama ‘Yan bindiga 7, kuma su ka kashe su a nan take.
Mun ji cewa kusan duka ‘Yan Majalisar Jihar Bauchi za su marawa Jam’iyyar APC baya a zaben da za ayi bayan da shugaban na APC a Bauchi Uba Nana yace sun cin ma matsayar yin na’am da zabin da APC tayi a makon nan.
Wani dan Najeriya ya janyo hankulan ma'abota amfani da kafafen sada zumunta bayan wani ya bayar da labarin bajintar da ya yi duk da kallubalen rashin lafiya da ya ke fama da ita. Wani mai ma'abocin dandalin sada zumunta mai suna M
Firai Ministar kasar Birtaniya Theresa May, a ranar Laraba ta fatattakin babban sakataren tsaro na gwamnatin kasa, Gavin Williamson, sakamakon takaddamar bayyanar wani rahoton sirri akan inganta harkokin sadarwar zamani na kasar.
A yayin ci gaba da fafutikar kawo karshen ta'addanci musamman garkuwa da mutane, sufeto Janar na 'yan sanda Muhammad Adamu, ya bayar da umurnin sauya kwamishinan 'yan sandan jihar Kaduna, CP Ahmed Abdulrahman.
Dubban ma'aikatan jihar Taraba da suka taru a filin motsa jiki na Jolly Nyame domin bikin ranar ma'aikata sun gamu da bacin rai sakamakon rashin bayyana matsayan gwamnatin jihar a kan batun biyan sabon albashi mafi karanci da mata
Da yawa daga cikin wasu yankunan Arewacin Najeriya na fuskantar matsanancin zafi da kuna ta dumamar rana cikin 'yan makonnin da suka gabata da a halin yanzu ake ci gaba da fargabar barkewar wasu nau'ikan cututtuka.
Farashin Burodi da sauran dangin kayan abinci da ake sarrafawa da fuklawa za su yi tashin doron zabuwa a kwana-kwanan nan cikin kasar nan ta Najeriya a sakamakon doriyar N600 akan farashin kowane buhu guda na fulawa da aka samu.
Wata kotun koli a garin Dutse, babban birnin jihar Jigawa ta yankewa wani mutumi mai shekaru 39 a duniya hukuncin kisa, bayan ta kama shi da hannu dumu-dumu da laifin satar mutane, da kuma laifin kisan kai...
Masu zafi
Samu kari