Siyasa mugun wasa: Atiku ya kalubalanci Buhari ya bayyana shaidar kammala karatunsa

Siyasa mugun wasa: Atiku ya kalubalanci Buhari ya bayyana shaidar kammala karatunsa

Wasa farin girki, inji Hausawa, babu abinda ba zaka ji ko ka gani ba a siyasar Najeriya, musamman idan rashin jituwa irin na bukata ya samu, inda zaka ji kowa na kokarin bankado sirrin abokin hamayyarsa da nufin sai ya kaishi kasa, haka siyasarmu ta gada.

Tsohon dan takarar shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya kalubalanci shugaban kasa Muhammadu Buhari daya bayyana takardun shaidan kammala karatunsa idan har da gaske yayi, kuma da gaske suna wajen rundunar Sojan kasa kamar yadda yake ikirari.

KU KARANTA; Gwamnoni na fakewa da matsalar tsaro suna satar kudaden al’umma – Inji Magu

Siyasa mugun wasa: Atiku ya kalubalanci Buhari ya bayyana shaidar kammala karatu
Atiku Buhari
Asali: Facebook

Atiku ya bayyana haka ne a cikin martanin daya shigar gaban kotun sauraron koke koken zabe, inda yace idan har da gaske Buhari yayi karatu, kuma takardunsa na wajen rundunar Sojan kasa kamar yadda yake cewa, toh ya umarcesu su bayyana takardun, shikenan magana ta wuce.

Lauyan Atiku, Livy Uzoukwu ne ya mika wannan korafi gaban kotun, inda yace Atiku ya mika ma hukumar INEC takardunsa a jikin fom CF001, don haka ya bukaci kotun ta tabbatar da Atiku a matsayin wanda ya lashe zaben 2019 tunda Buhari bai mika ma INEC nasa takardun ba.

Atiku ya cigaba da fadin cewa duk wasu kwasa kwasai da samun horo da Buhari yake ikirarin ya halarta ko ya samu har yake ganin ya sha gaban Atiku dasu ba zasu taba maye gurbin shaidun kammala karatu ba, kuma ba sune abinda INEC ta nema ba.

Idan za’a tuna a kwanakin baya ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ta hannun lauyoyinsu suka shaida ma kotun cewa Atiku ba dan Najeriya bane, asalinsa dan Kamaru ne, kuma Buhari ya fishi ba sa’anshi bane sakamakon Difloma kadai yake dashi.

Sai dai Legit.ng ta ruwaito har yanzu kotun bata sanya ranar da za’a fara zaman sauraron korafe korafen abokan hamayyar da suka fafata a zaben shugaban kasar Najeriya na ranar 23 ga watan Feburairun shekarar 2019 ba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel