Gwamnan Taraba ya yi gum game da batun biyan sabon mafi karancin albashi na N30,000

Gwamnan Taraba ya yi gum game da batun biyan sabon mafi karancin albashi na N30,000

Dubban ma'aikatan jihar Taraba da suka taru a filin motsa jiki na Jolly Nyame domin bikin ranar ma'aikata sun gamu da bacin rai sakamakon rashin bayyana matsayan gwamnatin jihar a kan batun biyan sabon albashi mafi karanci da mataimakin gwamnan jihar, Haruna Manu bai yi ba.

Haruna Manu wanda ya wakilci gwamnan jihar Darius Ishaku a wurin taron ya ki cewa uffan a kan batun biyan sabon albashi mafi karanci na N30,000 da galibin jihohi suka yi alkawarin za su fara biya.

Sai dai ya yabawa ma'aikatan jihar Taraba bisa goyon bayan da suka bawa gwamnan jihar ta hanyar jefa masa kuri'u da ya bashi nasarar lashe zabe karo na biyu.

Gwamnan Taraba ya yi gum game da batun biyan sabon mafi karancin albashi na N30,000
Gwamnan Taraba ya yi gum game da batun biyan sabon mafi karancin albashi na N30,000
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Tsallake rijiya da baya: Abubuwa 5 da ya kamata ku sani a kan Zainab Aliyu

Mataimakin gwamnan ya kuma taya shugabanin kungiyar Kwadago (NLC) na jihar murnar gudanar da zabukkan su cikin lumana da zaman lafiya.

Shugaban kungiyar Kwadago na jihar, Kwamared Peter Gambo ya yi kira ga gwamnatin jihar ta kaddamar da sabon albashi mafi karanci na N30,000 ga ma'aikatar jihar.

Kwamared Gambo ya kuma bukaci gwamnatin jihar ta Taraba ta biya malaman makarantu da ma'aikatan kananan hukumomi albashinsu na watanni uku da suke bi bashi.

Shugaban na kungiyar Kwadagon ya kuma yi kira da gwamnatin jihar ta fara daukan sabbin ma'aikata duba da cewa akwai bukatar maye gurbin wadanda su kayi murabus cikin gaggawa.

A wani rahoton, Legit.ng ta kawo muku cewa gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje ya yiwa ma'aikatan jihar alkawarin cewa zai fara biyan sabon albashin mafi karanci ga ma'aikatan jihar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel