‘Yan Majalisar Jihar Bauchi za su marawa Jam’iyya baya - APC

‘Yan Majalisar Jihar Bauchi za su marawa Jam’iyya baya - APC

Mun samu labari cewa takarar Sanata Ahmad Lawan da Honarabul Femi Gbajabiamila ta kara samun karfi bayan da ‘Yan majalisar Bauchi su ka sha alwashin goyon bayan su a zaben bana da za ayi.

Sanatoci 3 da aka zaba daga jihar Bauchi da kuma Takwaransu 11 daga majalisar wakilai na jihar za su bada cikakkiyar mubaya’ar su ga wadanda jam’iyyar APC mai mulki ta zaba su rike majalisar tarayyar kasar a zaben na 2019.

Ana sa rai ‘Yan majalisan na Bauchi da su ka lashe zabe a karkashin jam’iyyar APC mai mulki za su marawa Ahmad Lawan da kuma Femi Gbajabiamila baya ne a zaben majalisar dattawa da na wakilan tarayya da za a yi a watan gobe.

Shugaban jam’iyyar APC na jihar Bauchi, Uba Ahmed Nana, ya bayyana cewa ‘yan majalisun da su ka fito daga Bauchi za su marawa tafiyar Ahmad Lawan da Femi Gbajabiamila baya ne domin ganin cigaban majalisar Najeriya.

KU KARANTA: Jam’iyyar APGA mai mulki a Anambra ta rasa wani babban 'Dan Majalisa

Uba Nana yace sun yanke shawara game da zaben majalisa na bana don haka su ka nemi ‘yan majalisar Bauchi su yi wa jam’iyyar APC biyayya, duba da cancantar wadanda jam’iyyar ta tsaida takara domin su rike majalisar tarayya a 2019.

Sanatocin da aka zaba a jihar su ne: Adamu Balkachuwa, Lawal Yahaya Gumau da kuma Halliru Dauda Jika. Haka kuma ‘yan majalisar tarayya na jihar sun hada da: Mansur Manu Soto, Tata Umar, da Hon. Garba Mohammed Gololo.

Sauran ‘yan majalisar da za su wakilci jihar a majalisa ta 9 sun hada da: Abdullahi Sa’ad Abdulkadir, Kani Abubakar Faggo; Umar Muda Lawal; Mashema Mohamed, da kuma Honrabaul Makama Misau.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel