Wani gurgu maras kafafu ya kammala digiri a ABU da sakamako mafi daraja
Wani dan Najeriya ya janyo hankulan ma'abota amfani da kafafen sada zumunta bayan wani ya bayar da labarin bajintar da ya yi duk da kallubalen rashin lafiya da ya ke fama da ita.
Wani mai ma'abocin dandalin sada zumunta mai suna Mahmoud Shuaib ne ya wallafa a shafinsa na Twitter cewar wani matashi mai suna Sani Khalid ya cire tuta a karantunsa na jami'a.
A cewar Shuaibu, matashin wadda gurgu ne mara kafafu ya kammala karatun digirinsa na farko daga tsangayar nazarin kimiyyar ababe masu rai (Biological Science) daga Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria.
"Ku sadu da Sani Khalid daga jihar Katsina wanda ya kammala digirinsa daga tsangayar kimiyyar ababe masu rai (Biological Science) daga ABU Zaria da maki 4.56 (Sakamako mai daraja na farko) duk da cewa shi gurgu ne maras kafafuwa. Ina maka fatan alheri; kai abin koyi ne ga al'umma. Ku taya ni watsa wannan labarin domin mu taya wannan hazikin murna." inji shi.
DUBA WANNAN: Ganduje ya yi alkawarin fara biyan ma'aikatan Kano sabuwar albashi
Wannan sakon da Shuaibu ya wallafa ya janyo hankulan mutane sosai inda suka rika tofa albarkacin bakinsu game da bajintar da matashin ya yi. Ga wasu daga cikin abubuwan da suka fadi a kasa.
A wani rahoton, Legit.ng ta kawo muku cewa wani yaro mai shekaru 12 a duniya, Joshua Beckford ya samu gurbin karatu a Jami'ar Oxford mai daraja a duniya domin fara karatunsa na digiri.
Wannan hazikin yara yana daya daga cikin yara da akayi itifakin yana daga cikin masu hazaka a duniya.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng