Kotu ta yanke wa wani barawon mutane hukuncin kisa a jihar Jigawa

Kotu ta yanke wa wani barawon mutane hukuncin kisa a jihar Jigawa

- Wata kotu a jihar Jigawa ta yankewa wani kasurgumin barawon mutane hukuncin kisa ta hanyar rataya

- Kotun ta kama mutumin da laifuka kala uku, wadanda suka hada da kisan kai, garkuwa da mutane da kuma ta'addanci

Wata kotun koli a garin Dutse, babban birnin jihar Jigawa ta yankewa wani mutumi mai shekaru 39 a duniya hukuncin kisa, bayan ta kama shi da hannu dumu-dumu da laifin satar mutane, da kuma laifin kisan kai.

Kotun ta kama Datti Buba, mazaunin karamar hukumar Giade dake jihar Bauchi, da laifin satar mutane da kuma kashe mutane biyu daga cikin wadanda ya sata din.

Kotun ta kama Datti da laifuka kala uku, haddin baki wurin aikata laifi, garkuwa da mutane da kuma kisan kai.

Kotu ta yanke wa wani barawon mutane hukuncin kisa a jihar Jigawa

Kotu ta yanke wa wani barawon mutane hukuncin kisa a jihar Jigawa
Source: Depositphotos

Alkalin kotun mai shari'a Ubale Ahmed, ya yankewa Mista Buba hukuncin kisa ta hanyar rataye, bisa laifin kashe mutane biyu da ya yi wadanda ya sata a jihar Jigawa.

Wanda ake tuhumar ya shaidawa kotu cewa shi da wasu mutane biyu, Adamu Sabo da Usman Idris, duka daga jihar Bauchi, suka aikata laifin.

KU KARANTA: Amarya ta haihu a daidai lokacin da ake daura mata aure

Kodayake, kotun ta amince da mutane biyun da Mista Buba ya lissafo, game da laifukan na su. Da yake yanke hukunci akan mai laifin, alkalin ya ce laifin ya sabawa sashi na 97,221 da kuma sashi na 273 na dokar kasa.

Bayan haka kuma kotun ta yankewa Mista Buba hukuncin shekara biyar a gidan yari bisa laifin ta'addanci, da kuma hukuncin shekara 10 bisa laifin garkuwa da mutane.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel