Tambuwal, Ambode, da Ishaku ba su ce uffan a game da kara albashi ba

Tambuwal, Ambode, da Ishaku ba su ce uffan a game da kara albashi ba

A Jihohin Legas, Osun, Taraba da kuma Sokoto, haka aka yi taron bikin Ranar Ma’aikata a Najeriya, ba tare da an san inda gwamnonin su ka sa gaba ba, a game da maganar karin albashin ma’aikata.

Daiky Trust ta rahoto cewa wasu daga cikin gwamnoni ba su bayyana inda su ka sa dosa ba a kan maganar kara albashin ma’aikatan gwamnati zuwa akalla N30, 000 duk wata. Daga cikin wadannan gwamnoni akwai na Legas.

Gwamna Akinwumi Ambode mai barin-gado bai fito ya bayyana niyyarsa na kara albashin ma’aikatan jihar Legas a lokacin da yayi jawabi wajen bikin murnar Rana ta ma’aikata da aka yi jiya Ranar Laraba 1 ga Watan Mayun nan ba.

Wani daga cikin kwamishinononin Akinwumi Ambode ne ya wakilce sa a taron da aka shirya a wannan rana. Haka zalika a jihar Osun, gwamna Gboyega Oyetola yayi gum da bakinsa a kan batun karin albashin a jawabinsa jiya.

KU KARANTA: Wani Gwamnan PDP ya bada sharadi kafin ayi karin albashi

Tambuwal, Ambode, da Ishaku ba su ce uffan a game da kara albashi ba

Gwamnonin wasu Jihohi sun yi bakkam a kan maganar kara albashi
Source: UGC

Kamar dai Ambode, gwamnan na Osun ya maida hankali ne wajen yin bayani game da yadda yake aikin da ke taimakawa ma’aikatan jihar. Ana sa rai a wannan wata ne Ma’aikata za su fara karbar sabon tsarin albashin da bai gaza N30, 000 ba.

A jihar Taraba da ke cikin Arewacin Najeriya, gwamnatin jihar ba ta furta kalma guda a kan abin da ya shafi sabon albashi a lokacin da aka yi taron bikin Ranar ma’aikata ba. Mataimakin gwamna, Haruna Manu shi ne yayi jawabi a taron.

Haka zalika ma’aikatan jihar Sokoto sun ji jikin su yayi sanyi yayin da gwamna Aminu Waziri Tambuwal, yayi jawabin sa ya gama bai ambaci batun karawa ma’aikata albashi ba. Buhari Bello Kware shi ne ya wakilci gwamna a taron.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel