Garkuwa da Mutane: IG na kasa ya sauya Kwamishinan 'yan sandan jihar Kaduna

Garkuwa da Mutane: IG na kasa ya sauya Kwamishinan 'yan sandan jihar Kaduna

A yayin ci gaba da fafutikar kawo karshen ta'addancin kashe-kashe, garkuwa da mutane da sauran miyagun laifuka na masu mummunar ta'ada, sufeto Janar na 'yan sanda Muhammad Adamu, ya bayar da umurnin sauya kwamishinan 'yan sandan jihar Kaduna, CP Ahmed Abdulrahman.

Domin ci gaba da zage dantsen ta wajen tabbatar da tsaro a fadin kasar musamman jihar Kaduna da sauran jihohin da annobar ta'addanci ta fi kamari, IG na kasa ya bayar da umurnin sauya kwamshinan 'yan sandan jihar Kaduna zuwa cibiyar leken asiri ta hukumar 'yan sanda da ke garin Abuja.

Sufeto Janar na 'yan sanda, Muhammad Adamu
Sufeto Janar na 'yan sanda, Muhammad Adamu
Asali: Twitter

Kwamishinan 'yan sanda na jihar Bauchi, CP Ali Ali Janga, zai karbi ragamar jagorancin hukumar ta tsaro a jihar Kaduna domin gwada irin ta sa bajintar da kuma dabaru wajen fuskantar kalubalai na rashin tsaro kamar yadda rahotanni suka bayyana.

Sauran kwamishinonin 'yan sanda da sauye-sauyen mukami da kuma wuraren aiki ya shafa sun hadar da; CP Habu Sani Ahmadu da zai kula da al'amurran tsaro a jihar Bauchi, CP Omololu Shamsudeen Bishi da zai karbi ragamar jagoranci a cibiyar miyagun laifuka ta jihar Legas.

KARANTA KUMA: Jerin jihohin Arewa 9 da ake fuskantar matsanancin zafi

CP Mukaddas Muhammad Garba, tsohon babban jami'in tsaro a ofishin bayar da shawarwari a kan harkokin tsaro na kasa reshen jihar Benuwai, zai karbi ragamar jagoranci ta kujerar kwamshinan 'yan sanda na jihar.

A yayin haka babban sufeton 'yan sanda na kasa, ya hori sabbin jagororin hukumar da sauye-sauyen wuraren aiki ya shafa da su jajirce tare da bayar da himma wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyan su na bayar da tsaro mai inganci ga al'umma.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel