An Shiga Tashin Hankali a Filato, Ƴan Bindiga Sun Kashe Gomman Mutane a Sabon Hari

An Shiga Tashin Hankali a Filato, Ƴan Bindiga Sun Kashe Gomman Mutane a Sabon Hari

  • Adadin mutanen da aka kashe a hare-haren da aka kai wa yankunan ƙaramar hukumar Barkin Ladi ya kai 10, ciki har da ɗan sanda ɗaya
  • Maharan sun kai hare-haren ne a lokaci guda a yankunan Sabon Layi, Rakung, Gangare, da kuma kusa da babban asibitin garin
  • Ƙungiyoyin matasa da na makiyaya ta Filato sun nuna fargaba kan yadda tsaro ke ƙara taɓarbarwa duk da kasancewar jami'an tsaro a yankin

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Filato - Rahotanni sun nuna cewa adadin mutanen da suka rasa rayukansu biyo bayan wasu hare-hare da aka kai wa wasu garuruwa a ƙaramar hukumar Barkin Ladi ta Jihar Filato ya tashi zuwa mutane 10.

Hare-haren, waɗanda aka ce wasu gungun 'yan ta'adda ne suka kai su a yammacin ranar Asabar, sun jefa mazauna yankunan Sabon Layi, Rakung, Gangare, da kewayen babban asibitin garin cikin matsananciyar fargaba.

Kara karanta wannan

Ana fargabar sabon harin sojoji ya kashe mutanen gari a jihar Neja

An kashe kalla mutane 10 a sabon harin da 'yan bindiga suka kai Filato.
Gwamna Caleb Mutfwang na jihar Filato cikin yanayin damuwa. Hoto: @CalebMutfwang
Source: Facebook

'Yan bindiga sun kashe 10 a Filato

Mazauna yankin sun bayyana cewa maharan sun buɗe wuta ba kakkautawa, lamarin da ya tilasta wa mutane da dama tserewa daga gidajensu domin tsira da rayukansu, in ji rahoton Vanguard.

Ibrahim Yusuf Babayo, shugaban ƙungiyar Miyetti Allah, ya tabbatar wa manema labarai a birnin Jos cewa an kashe makiyaya uku a cikin wannan harin.

Wani mazaunin garin mai suna Livinus Pam ya bayyana cewa:

“Zuwa safiyar Lahadi, an gano gawarwaki 10 daga wurare daban-daban da harin ya shafa, inda aka kai wasu ɗakin ajiyar gawa, yayin da mutane shida da suka ji rauni ke karɓar magani a asibitoci.”

Kungiya ta koka kan rashin tsaro

Ƙungiyar matasan Berom (BYM) ta nuna damuwa kan taɓarbarar tsaro a Barkin Ladi duk da yawan jami'an tsaro da shingen bincike a yankin, in ji rahoton Punch.

Cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labarai na ƙungiyar, Rwang Tengwong ya sanya wa hannu, ƙungiyar ta sake nanata rashin amincewarta da kwamandan rundunar Operation Enduring Peace (OPEP).

Kara karanta wannan

Fada ya barke tsakanin kungiyoyin 'yan bindiga a Zamfara, an kashe hatsabibin jagora

Ƙungiyar ta yi zargin cewa mazauna yankin yanzu suna rayuwa ne cikin tsoro da firgici domin maharan suna yawo yadda suka ga dama ba tare da an takaita su ba.

'Yan ta'adda sun farmaki garuruwan Filato suka kashe mutane masu yawa
Taswirar jihar Filato inda 'yan ta'adda suka kashe akalla mutane 10. Hoto: Legit.ng
Source: Original

Kiran kafa ma'aikatar tsaron cikin gida

Sakamakon waɗannan hare-hare, ƙungiyar ta BYM ta yi kira ga gwamnati da ta kafa "Ma'aikatar Tsaron Cikin Gida da Ayyukan Jinƙai" domin haɗa kai wajen samar da tsaro da kuma ba wa waɗanda harin ya shafa agajin gaggawa.

Ƙungiyar ta buƙaci gwamnatin tarayya da ta jihar Filato, tare da hukumomin tsaro, da su ɗauki matakin gaggawa na gaske domin kawo ƙarshen waɗannan tashe-tashen hankula da suka addabi yankunan.

An kashe mutane 13 a Filato

A wani labari, mun ruwaito cewa, akalla mutane 13 ne aka kashe, ciki har da mata masu juna biyu a wani harin dare da aka kai ƙauyen Ngbra Zongo a ƙaramar hukumar Bassa.

A wani harin daban da ya faru a ƙaramar hukumar Barkin Ladi, an rahoto cewa 'yan bindiga sun kashe akalla mutane biyar tare da raunata wasu uku.

Garuruwan Filato da abin ya shafa sun nuna damuwa kan yadda hare-haren ke yawaita, inda suka roki jami'an tsaro da su ƙara kaimi wajen kare rayukansu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com