SDP 2027: Jam’iyyar Adawa Ta Farko Ta Tsaida Ɗan Takarar Shugaban Kasa

SDP 2027: Jam’iyyar Adawa Ta Farko Ta Tsaida Ɗan Takarar Shugaban Kasa

  • Jam’iyyar SDP da ke adawa a Najeriya ta amince da fitar da daya daga cikinta jiga-jiganta a matsayin dan takararta na shugaban kasa
  • Wanda aka tsayar, Adewole Adebayo ya soki manufofin tattalin arzikin gwamnati, yana cewa sun jefa ‘yan Najeriya cikin wahala tare da sanya masu aiki tukuru
  • Sabon shugaban SDP na kasa, Sadiq Gombe, ya yi alkawarin samar da sahihin shugabanci tare da inganta jam’iyyar

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Jam’iyyar SDP mai adawa a Najeriya ta bayyana wanda zai tsaya mata takarar shugaban kasa a zaben shekarar 2027.

Jam'iyyar SDP ta zabi Adewole Adebayo a matsayin dan takararta a zaben 2027 bayan cimma matsayar hadin kai a taron kasa da aka gudanar a Bauchi.

SDP ta fitar da dan takara da zai kara da Tinubu
Shugaba Bola Tinubu da dan takararjam'iyyar SDP, Adewle Adebayo. Hoto: Bayo Onanuga, SDP Nigeria.
Source: Twitter

Da yake jawabi yayin taron, Adebayo ya bayyana cewa matsin tattalin arziki da manufofin gwamnati sun jefa talakawa cikin mawuyacin hali duk da kokarin da suke yi wajen neman rayuwa, cewar TheCable.

Kara karanta wannan

Ta fara tsami a Kebbi tsakanin Gwamna da Malami bayan sayan fom din takara

NDC ta tura tikitin takara Kudu

Hakan na zuwa ne kwana daya bayan jam'iyyar NDC ta tura tikitin takarar shugaban kasa zuwa Kudancin Najeriya.

Daman Sanata Rabiu Kwankwaso ne da Peter Obi suke kan gaba a neman tikitin takarar kafin matakin jam'iyyar.

Daga bisani, Rabiu Kwankwaso ya yi mubaya'a ga matakin jam'iyyar inda ya ce zai goyi bayansa har zuwa ga nasarar zabe.

Kamar SDP, jam'iyyar NDC ta yi taro kan tikitin takarar shugaban kasa
Jiga-jigan NDC, Peter Obi, Seriake Dickson da Rabiu Musa Kwankwaso. Hoto: Mr. Peter Obi.
Source: Twitter

SDP ta tsayar da dan takara

Taron ya kuma tabbatar da Sadiq Gombe a matsayin shugaban jam’iyyar na kasa, bayan amincewar shugabanni da wakilan jam’iyyar daga jihohi daban-daban.

Adebayo ya ce iyaye da dama na kasa samar da abinci, biyan kudin makaranta da kuma kula da marasa lafiya saboda halin matsin rayuwar da ake ciki.

Dan takarar shugaban kasar ya kuma yi magana kan wahalhalun da wasu ‘yan Najeriya ke sha a kasashen waje domin neman abin rayuwa.

Ya ce:

“Ga mutane da dama da ke aiki tukuru, manufofin tattalin arzikin gwamnati mai ci sun sanya su zama kamar kasalai, domin idan suka koma gida, ‘ya’yansu suna tambayar dalilin da ya sa babu abinci, me ya sa ba a biya kudin makaranta ba, da kuma dalilin da ya sa marasa lafiya a iyali ba sa samun kulawar lafiya.”

Kara karanta wannan

2027: Sanatan APC a Gombe ya sauya sheka zuwa PDP bayan rasa tikitin takara

Adebayo ya gargadi ‘yan Najeriya kan abin da ya kira yunkurin mayar da kasar karkashin jam’iyya daya, yana mai kira ga jama’a su yi amfani da tsarin dimokuradiyya domin kawo canji.

Shi ma Usman Bugaje ya soki matsalar tsaro, tsadar mai, rashin aikin yi da talauci, yana zargin jam’iyya mai mulki da kokarin takaita sararin siyasa da murkushe adawa.

Gwamna ya amince da zaben kato bayan kato

An ji cewa Gwamna Mai Mala Buni ya bayyana cewa jam’iyyar APC a Jihar Yobe za ta yi zaben ƙato bayan ƙato idan har ba a cimma matsayar bai-daya kan dan takara ba.

Masu neman takarar gwamna shida sun yi watsi da zaman sulhu da wasu jiga-jigan jam’iyyar suka yi na tsayar da Alhaji Baba Wali matsayin ɗan takara.

Gwamnan ya nanata cewa hadin kan jam’iyyar shi ne babban burinsa, kuma za su ci gaba da tattaunawa da wadanda zabin Wali bai yi wa daɗi ba don neman mafita.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com