Tsugono ba Ta Ƙare ba: Amurka da Iran Sun Ƙi Amincewa da Sharuddan Sulhu
- Shugaban Amurka Donald Trump ya ƙi tayin da Iran ta miƙa kan kawo ƙarshen yaƙin Gabas ta Tsakiya bayan sharuddan da kasarsa ta aika
- Iran ta ce ba za ta miƙa wuya ga sharuddan da Amurka ta fara aika mata ba, yayin da ta nemi diyya da buƙatar a cire mata takunkumi
- Rikicin ya ƙara jefa kasuwar makamashi cikin ruɗani tare da hana zirga-zirga ta Hormuz da a yanzu haka kasashen biyu suka garƙame
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
United States – Shugaban Amurka, Donald Trump, ya bayyana cewa tayin da Iran ta gabatar domin kawo ƙarshen yaƙin da aka shafe makonni 10 ana yi a Gabas ta Tsakiya abin ƙi ne gaba ɗaya.

Kara karanta wannan
Yakin Iran da Isra'ila: An 'gano' kasar da tafi cin moriyar rikicin fiye da Amurka
Sakon Trump na zuwa ne bayan ƙasarsa ta mika tayin kawo karshen yakin ga Iran ta hannun kasar Pakistan da ke shiga tsakani domin a sasanta.

Source: Getty Images
A ruwayar kafar BBC, martani da Iran ta yi game da tayin Amurka bai yi shugaba Donald Trump daɗi ba, inda ya ce ba zai aminta da hakan ba sam.
Trump ya yi watsi da tayin Iran
CNBC ta wallafa cewa shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da cewa ya karanta dukkannin martani da Iran ta yi ga tayinsa.
Ya ce:
“Na karanta martanin da waɗanda ake kira wakilan Iran suka bayar. Ban ji daɗinsa ba — abin ƙi ne gaba ɗaya!”
Kafofin yaɗa labaran gwamnatin Iran sun bayyana martanin Tehran a matsayin ƙin amincewa da tayin Amurka, wanda suka ce yana kama da buƙatar miƙa wuya.
A cikin martanin nata, Iran ta buƙaci a biya ta diyya saboda yaƙin, a ba ta cikakken iko kan mashigar ruwa na Hormuz wanda ta cikin ƙasar ta ratsa.
Wasu daga cikin bukatun Iran
Sanarwar ta kara da cewa kasar Iran ta nemi a cire mata takunkumin tattalin arziki, tare da sakin kadarorinta da aka daskarar da su.
Shugaban Iran, Masoud Pezeshkian, ya yi tsayin daka yayin da ake ci gaba da tattaunawa, inda ya nanata cewa ba za su taɓa mika wuya ba.

Source: Getty Images
A kalaman shugaban:
“Ba za mu taɓa miƙa da kai ga maƙiyi ba, kuma idan aka yi maganar tattaunawa ko sulhu, hakan ba yana nufin miƙa wuya ko ja da baya ba ne.”
Rahotanni sun bayyana cewa Iran ta ƙi buƙatar Amurka kan shirinta na nukiliya da kuma ajiyar sinadarin haɗa makamin, wato uranium.
Maimakon haka, Tehran ta ba da shawarar a yi tattaunawa daban-daban, sannan ta amince ta rage ƙarfin wasu uranium ɗinta tare da aika sauran zuwa wata ƙasa daban.
Amurka na son Iran ta kawo ƙarshen shirinta na nukiliya a matsayin wani ɓangare na yarjejeniyar zaman lafiya lamarin da har yanzu aka gaza cimma wa.
Barazanar Iran ga Amurka
A baya, mun kawo labarin cewa rundunar IRGC ta Jamhuriyar Musulunci a Iran ta yi barazanar kai munanan hare-hare kan sansanonin Amurka da jiragen ruwa.
Iran ta yi wannan gargadi ne ga kasar idan ta kai hari kan tankokin mai ko jiragen kasuwancin kasar wanda ka iya jawo martani mai zafi daga dakarunta.
Rikicin Iran da Amurka tare da Isra’ila ya kara tsananta bayan hare-haren da aka kai tun watan Fabrairu, 2026 lamarin da ya haddasa martanin Tehran da rikicin mashigar Hormuz.
Asali: Legit.ng
