Sabbin bayanai sun bayyana akan yadda barayi suka yi garkuwa da Magajin garin Daura

Sabbin bayanai sun bayyana akan yadda barayi suka yi garkuwa da Magajin garin Daura

Wasu sababbin bayanai sun bayyana dangane da yadda gungun yan bindiga suka afka cikin garin Daura, har suka yi awon gaba da Magajin garin Daura, Alhaji Musa Umar Uba, da yammacin ranar Laraba, 1 ga watan Mayu bayan sallar Magariba.

Shi dai Magajin gari shahararren attajiri ne daya taba kasancewa kwanturola a hukumar yaki da fasa kauri ta kasa, watau kwastam, kanin Sarkin Daura ne, surukin shugaban kasa Muhammadu Buhari ne sakamakon yana auren Hajiya Bilki, diyar yayar Buhari Hjiyar Rakiya, sa’annan diyarsa Fatima na auren babban dogarin Buhari, Kanal Mohammed Abubakar.

KU KARANTA: Gwamnoni na fakewa da matsalar tsaro suna satar kudaden al’umma – Inji Magu

Sabbin bayanai sun bayyana akan yadda barayi suka yi garkuwa da Magajin garin Daura
Magajin garin Daura Musa Umar Uba
Asali: UGC

Majiyar Legit.ng ta ruwaito wasu shaidun gani da ido sun bayyana yadda lamarin ya auku, tun daga tsayuwar yan bindigan a kofar gidan Magaji, fitowarsu daga mota, zuwa daukeshi, har zuwa yadda suka yi awon gaba dashi.

Wani da abin ya faru a gabanshi, Malam Abdullahi yace “A cikin motoci biyu suka zo, Toyota Hilux da wata Pijo 406, sun tarar da Magaji a gaban gidansa dake kwanar Agam tare da jama’a bayan munyi sallar Magariba, kai tsaye suka yi kansa, yayin da guda ya dinga harbi a sama, da haka suka tursasa mai shiga motar, suka arce dashi.”

Sai dai jama’ da dama sun shaida cewa Magajin gari baya komawa cikin gida bayan sallar magariba, don haka yake zama a kofar gidansa tare da jama’ansa har sai sun yi sallar Isha’I, wannan ya baiwa yan bindigan daman samunsa cikin sauki.

Wani makwabcin Magaji, mai suna Malam Muhammad ya bayyana cewa “Kafin zuwan barayin, an jiyo Magaji yanata amsa waya, da alama wasu mutane sun fada masa suna hanyar zuwa ganinsa a gida, ai kuwa zuwansu keda wuya suka kamashi suka shigar cikin mota suka tsere.”

Duk da cewa jama’a sun razana, amma wasu sunyi karfin halin kokarin kubutar da Magajin gari, amma sai guda daga cikin yan bindigan ya bude wuta a sama, daga nan kowa yayi ta kansa, sai dai an tabbatar hanyar Zangon Daura suka bi dashi.

Bayan aukuwar lamarin an hangi daruruwan jama’a sun taru a kofar gidan Magajin suna jimami tare da alhinin abinda ya sameshi, sa’annan jami’an rundunar Soja da Yansanda sun yi ta gudanar da sintiri a cikin garin Daura.

Wani dan uwa na jini ga Magajin gari yace har yanzu yan bindigan basu tuntubi iyalansa ba, sa’annan duk kokarin da aka yin a kiran wayoyinsa ya ci tura sakamakon barayin sun kashe wayoyin nasa gaba daya.

Kaakakin masarautar Daura, Usman Ibrahim da shugaban riko na karamar hukumar Daura Abba Mato duk sun tabbatar da aukuwar lamarin, sai dai Mato yace jami’an tsaro sun bazama farautar yan bindigan tare da kokarin ceto Magajin gari.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel