'Yan bindiga sun kai hari makarantar sakandare ta mata a jihar Zamfara

'Yan bindiga sun kai hari makarantar sakandare ta mata a jihar Zamfara

- 'Yan bindiga sun kai wani mummunan hari makarantar sakandare ta mata a jihar Zamfara

- Rahotanni sun nuna cewa 'yan bindigar sun sace malamai biyu da wasu mata guda hudu

- 'Yan bindigar ba su samu damar kai wa inda daliban makarantar suke bacci ba

Wasu masu garkuwa da mutane dauke da manyan bindigogi sun kai hari wata makarantar sakandare ta mata da ke jihar Zamfara, sun sace 'yammata masu yawan gaske wadanda har yanzu ba a san adadinsu ba.

Barayin sun kai samamen ne wata makarantar sakandare ta mata a wani gari mai suna Moriki da ke cikin karamar hukumar Zurmi, 'yan bindigar sun kai harin ne da daddare a lokacin da hankalin mutanen garin ya ke kan kallon wasan kwallon kafa na zakarun turai, kamar dai yadda wani mazaunin garin ya shaidawa manema labarai.

'Yan bindiga sun kai hari makarantar sakandare ta mata a jihar Zamfara
'Yan bindiga sun kai hari makarantar sakandare ta mata a jihar Zamfara
Asali: Twitter

Mutumin ya ce 'yan bindigar sun yi ta harbe harbe da suka shiga garin, inda suka kashe mutum daya.

Wani mutumi dan kungiyar sa kai da ke garin na Moriki ya bayyana cewa, 'yan bindigar tun yamma suka hana shige da fice a hanyar garin na Moriki, inda daga baya kuma suka kai hari garin da daddare.

KU KARANTAA: Masu garkuwa da mutaane sun bayyana dalilan da yasa suke satar mutane a kasar nan

Mutumin ya ce 'yan bindigar sun sace malaman makarantar guda biyu, sannan sun dauki mata masu dafawa daliban abinci guda hudu, sai dai kuma barayin ba su samu nasarar kai wa inda daliban suke bacci ba.

Barayin mutane dai a jihar Zamfara suna cin karen su babbaka, duk da kokarin da hukumomin tsaron Najeriya ke yi wurin ganin sun kawo karshen ta'addanci a yankin, amma har yanzu abin yaci tura.

Mutane masu dumbin yawa sun rasa rayukansu, inda yara da matan aure da yawa suka zama marayu da zawarawa dalilin rikicin da ke faruwa a fadin jihar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel