Yanzu Yanzu: Mahukunta a kasar Saudiyya sun sako Ibrahim Abubakar

Yanzu Yanzu: Mahukunta a kasar Saudiyya sun sako Ibrahim Abubakar

Kwana guda bayan sakin Zainab Habibu Aliyu da aka tsare a Saudiyya bisa zargin safarar miyagun kwayoyi, mahukunta kasar sun sake sakin wani mutum mai suna Ibrahim Abubakar wadda shima ya kasance a tsare.

An mika Abubakar a hannun wakilin ofishin jakadancin Najeriya, Jeddah Garba kamar yadda TVC News ta ruwaito.

Yanzu Yanzu: Mahukunta a kasar Saudiyya sun sako Ibrahim Abubakar
Yanzu Yanzu: Mahukunta a kasar Saudiyya sun sako Ibrahim Abubakar
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Tsallake rijiya da baya: Abubuwa 5 da ya kamata ku sani a kan Zainab Aliyu

An tsare Ibrahim Abubakar ne bisa zarginsa da safarar miyagun kwayoyi zuwa kasar mai tsarki kamar yadda ya faru da Zainab Aliyu.

Dokokin kasar Saudiyya sun tanadi hukuncin kisa ne ga duk wanda aka samu da laifin safarar miyagun kawayoyi zuwa kasar.

Kuma a a baya-bayan nan ne mahukunta kasar Saudiyyar suka yanke hukuncin kisa ga wata 'yar Najeriya da aka kama da laifin safarar miyagun kwayoyi a kasar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel