Tsadar Fulawa: Farashin Burodi zai tashi a Najeriya

Tsadar Fulawa: Farashin Burodi zai tashi a Najeriya

Akwai yiwuwar farashin Burodi da sauran dangin kayan abinci da ake sarrafawa da fulawa za su yi tashin doron zabuwa a kwana-kwanan nan cikin kasar nan ta Najeriya a sakamakon doriyar N600 akan farashin kowane buhu guda na fulawa da aka samu.

Kamfanonin sarrafa alkama sun kara Naira dari shida a kan farashin kowane buhu guda na Fulawa tun a watan Maris da ya gabata. Hakan ya sanya buhunan Fulawa da farashin su ya ke a kan N10,200 da kuma N11,300 su ka koma N10,700 da kuma N11,900.

Tsadar Fulawa: Farashin Burodi zai tashi a Najeriya
Tsadar Fulawa: Farashin Burodi zai tashi a Najeriya
Asali: UGC

Yayin ganawar sa da manema labarai ta hanyar wayar salula a birnin Maiduguri, Dominic Daniel Tumba Turi, shugaban kungiyar masu gashin dangin kayan abinci na Fulawa, ya ce doriyar farashin ya zo ne kwatsam ba tare da kamfanonin sarrafa alkama sun ankarar da su ba.

Da ya ke ci gaba da babatu na bayyana rashin jin dadin sa, Tumba ya ce tashin farashin Fulawa ya sanya kamfanoni da dama masu gashin Burodi da dangin kayan abinci na Fulawa sun dakatar da harkokin su na gudanarwa tare da rufe ma'aikatun su.

KARANTA KUMA: An sace Shanu fiye da 300 a jihar Filato

Ya yi kira na neman gwamnatin tarayya da ta yi gaggawar shiga cikin wannan lamari na karya farashin Fulawa da a cewar sa muddin ba haka ba, dole farashin Burodi da dangogin sa za su tashi a fadin kasar nan.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel