Najeriya da Moroko Sun Kulla Sabuwar Yarjejeniya, Ta Shafi Manyan Bangarori 3

Najeriya da Moroko Sun Kulla Sabuwar Yarjejeniya, Ta Shafi Manyan Bangarori 3

  • Najeriya da Maroko sun amince su sanya wa yarjejeniyar gina bututun iskar gas na NMGP hannu a ƙarshen shekarar 2026 da muke ciki
  • Ministocin ƙasashen biyu sun tattauna hanyoyin haɗin gwiwa a fannin samar da taki don tabbatar da wadatar abinci a Afirka
  • Ana shirin farfaɗo da Majalisar Kasuwanci ta ƙasashen biyu domin amfana da damar kasuwanci ta bai-ɗaya ta nahiyar Afirka (AfCFTA)

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Ministar Harkokin Wajen Najeriya, Amb. Bianca Odumegwu-Ojukwu, ta gudanar da tattaunawa mai amfani ta wayar taraho da takwaranta na Maroko, Nasser Bourita.

Ministocin biyu sun jaddada aniyarsu ta ƙarfafa haɗin gwiwa a fannonin da suka shafi moriyar juna, musamman aikin bututun iskar gas na Najeriya da Maroko (NMGP), wanda kuma ake kira da AAGP.

Najeriya da Moroko sun kulla yarjejeniya.
Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Sarki Mohammed VI na Moroko. Hoto: Carlos R. Alvarez/WireImage / Getty Images
Source: Getty Images

Najeriya da Moroko sun kulla alaka

Kara karanta wannan

Masu neman takara 6 sun hakura, an bar wa Shekarau tikitin sanatan Kano ta Tsakiya

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa, ma'aikatar harkokin wajen Najeriya ta sanar da cewa:

"Bayan kammala binciken fasaha na farko da hukumomin da abin ya shafa suka yi, ana sa ran Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Mai Martaba Sarki Mohammed VI za su sanya wa yarjejeniyar gwamnatocin biyu hannu a kwata na ƙarshe na shekarar 2026."

Baya ga batun makamashi, ɓangarorin biyu sun tattauna damar haɗin gwiwa wajen samar da taki da rarraba shi, ganin mahimmancin hakan ga wadatar abinci a Afirka.

Najeriya kuma tana nazarin karɓar baƙuncin zaman tattaunawa na biyu na Kwamitin Haɗin Gwiwa tsakanin ƙasashen biyu (JC) domin farfaɗo da yarjejeniyoyin da aka sanya wa hannu tun a shekarar 2018 lokacin tsohon Shugaba Muhammadu Buhari.

Muhimmancin kasuwancin Najeriya, Moroko

Ministocin sun nuna mahimmancin sake kafa Majalisar Kasuwanci ta Najeriya da Maroko, in ji rahoton Punch.

Wannan zai zama babban dandali na haɓaka kasuwanci tsakanin ƙasashen biyu, tare da amfani da damar da Yarjejeniyar Kasuwanci ta Afirka (AfCFTA) da kuma yarjejeniyar kauce wa haraji biyu tsakanin ƙasashen biyu suka samar don bunƙasa tattalin arziƙi.

Kara karanta wannan

An shiga tashin hankali a Filato, ƴan bindiga sun kashe gomman mutane a sabon hari

Minista Odumegwu-Ojukwu ta nuna godiyarta ga takwaranta na Maroko saboda gayyatar da ya yi mata na ziyarar aiki a Masarautar Maroko a lokacin da ya dace.

Minista Bianca Odumegwu-Ojukwu ta gode wa Mokoro kan gayyatar ziyarar aiki da kasar ta yi mata.
Ministar harkokin wajen Najeriya, Bianca Odumegwu-Ojukwu a dakin taron ma'aikatarta a Abuja. Hoto: @Ojukwu_Bianca
Source: Twitter

Kyautata alakar Najeriya da Moroko

Ana sa ran wannan ziyara za ta ƙara ƙarfafa alaƙar diplomasiyya da kuma ciyar da hangen nesa na haɗin gwiwa mai ƙarfi tsakanin ƙasashen biyu gaba don ci gaban nahiyar Afirka baki ɗaya.

Wannan tattaunawa ta nuna cewa Najeriya tana ƙara faɗaɗa hulɗarta da ƙasashen arewacin Afirka, inda take neman abokan haɗin gwiwa masu ƙarfi don magance matsalolin tattalin arziki da makamashi da suka addabi nahiyar.

Tinubu ya tura sakon jaje ga Moroko

A wani labari, mun ruwaito cewa, sama da mutane 600 suka mutu a wata mummunar girgizar kasa mai karfin awo 6.8 da ta afku a kasar Moroko.

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya jajantawa Sarkin Morocco Mohammed VI kan wannan lamari mai ban tausayi.

Tinubu ya tabbatarwa kasar ta Moroko goyon bayan Najeriya yayin da suke cikin aikib sake ginawa da kuma fitowa da karfi fiye da kowane lokaci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com