Donald Trump Zai Kwace Sinadaran Nukiliyar Iran, Ya Fadi Shirin da Ya Yi

Donald Trump Zai Kwace Sinadaran Nukiliyar Iran, Ya Fadi Shirin da Ya Yi

  • Shugaba Donald Trump ya bayyana cewa Amurka za ta kwace kayan nukiliyar Iran, yana mai cewa rundunar Space Force na sanya ido kanta
  • Trump ya yi barazanar cewa duk wanda ya kusanci wuraren nukiliyar Iran za a gano shi nan take, tare da daukar matakin soja cikin gaggawa
  • Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya ce har yanzu akwai sauran sinadarin uranium a Iran, yana mai jaddada cewa dole a cire su gaba daya

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Washingtn DC, US - Shugaban Amurka Donald Trump ya sha alwashin cewa kasarsa za ta kwace sauran kayan nukiliyar Iran.

Majiyoyi suka ce Trump ya bayyana cewa rundunar Space Force tana sanya ido sosai kan cibiyoyin nukiliyar Tehran daga sararin samaniya.

Amurka ta sha alwashin ruguza lamuran Iran
Shugaban kasar Iran, Masoud Pezeshkian da Donald Trump na Amurka. Hoto: Anadolu Ajansi, Donald J Trump.
Source: Getty Images

Trump ya bayyana hakan ne a wata hira da shirin “Full Measure with Sharyl Attkisson” da New York ta bibiya.

Kara karanta wannan

Shugaban sojin Iran ya gana da Mojtaba Khamenei, an ji abin da suka tattauna

Yadda Amurka ke sa ido a lamuran Iran

Shugaban ya ce Amurka tana sa ido sosai kan wuraren da ake adana sinadarin 'uranium' da aka tace a Iran.

Trump ya bayyana cewa fasahar sa ido ta Amurka na iya gano duk wanda ya kusanci wuraren cikin kankanin lokaci.

Shugaban ya yi gargadin cewa idan wani ya kusanci wuraren nukiliyar Iran, Amurka za ta gano shi tare da kai masa hari cikin gaggawa.

A lokacin rikicin Iran, Trump ya bayyana cewa ya yi tunanin tura dakarun kasa domin kwace kayan nukiliyar Iran, amma har yanzu bai bayar da umarnin aiwatar da hakan ba.

Tun farko dai Amurka ta kai hare-hare kan manyan cibiyoyin nukiliyar Iran guda uku a watan Yuni yayin Operation Midnight Hammer.

Sai dai wakilin musamman na Amurka Steve Witkoff ya bayyana cewa Iran har yanzu tana da isasshen sinadarin uranium da zai iya samar da makaman nukiliya har guda 11 idan aka kara tace shi.

Netanyahu ya magantu kan nukiliyar Iran
Firayim ministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu. Hoto: Benjamin Netanyahu.
Source: Facebook

Netanyahu ya magantu kan nukiliyar Iran

Kara karanta wannan

Amurka ta kai harin ba zata Iran, Trump ya yi karin haske kan tsagaita wuta

Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu ya ce har yanzu akwai sauran kayan nukiliya a Iran duk da hare-haren da aka kai.

“Har yanzu akwai sauran sinadarin 'uranium' da aka tace da dole a cire daga Iran.”

- Netanyahu ya fada yayin wata hira da CBS News.

Trump ya kuma zargi Iran da karya alkawari a tattaunawar sulhu, yana mai cewa gwamnatin Tehran na yin yarjejeniya sannan daga baya ta karya ta.

Ya ce Iran ta yi rauni sosai ta fuskar soja, yana mai cewa kasar ba ta da karfin ruwa, jiragen sama ko kariyar sararin samaniya kamar yadda take da su a baya.

Trump ya kara da cewa idan Amurka ta janye yanzu, Iran za ta dauki shekaru masu yawa kafin ta sake gina karfin sojinta.

Iran ta gargadi Amurka kan jiragen ruwanta

An ji cewa rundunar IRGC ta Jamhuriyar Musulunci a Iran ta yi barazanar kai munanan hare-hare kan sansanonin Amurka da jiragen ruwa.

Iran ta yi wannan gargadi ne ga kasar idan ta kai hari kan tankokin mai ko jiragen kasuwancin kasar wanda ka iya jawo martani mai zafi.

Rikicin Iran da Amurka tare da Isra’ila ya kara tsananta bayan hare-haren da aka kai tun watan Fabrairu, lamarin da ya haddasa martanin Tehran da rikicin mashigar Hormuz.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com