Sheikh Gumi Ya Dura a kan Amurka, Ya Zarge Ta da Rura Rashin Tsaro a Najeriya
- Fitaccen Malamin addinin musulunci, Sheikh Ahmad Gumi ya zargi hukumomin leƙen asirin Amurka da hannu a ta’addanci da ayyukan ‘yan bindiga a Najeriya
- Malamin ya yi zargin ne yayin martani ga Mike Arnold, fitaccen 'dan Amurka da ya sako Najeriya a gaba kan batun kashe Kiristoci da gan-dan a sassan kasar
- Martanin Sheikh Ahmad Gumi na zuwa ne a lokacin da Najeriya da Amurka ke ƙara haɗa kai wajen yaƙi da matsalar tsaro da kuma karfafa alaka a bangaren
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa. Jihar Kano – Fitaccen malamin addinin Musulunci da ke Kaduna, Ahmad Gumi, ya yi zargin cewa hukumomin leƙen asirin Amurka na da hannu wajen ɗaukar nauyin ayyukan ‘yan bindiga da mayaƙan Boko Haram a Najeriya.

Kara karanta wannan
Dan majalisar Amurka ya harzuka kan harin Plateau, ya gayawa Trump matakin dauka kan Najeriya
Fitaccen malamin ya bayyana haka ne a lokacin da Amurka ke maganganu game da zargin cewa ana yi wa kiristoci kisan kare dangi a kasar nan.

Source: Facebook
Sheikh Gumi ya bayyana hakan ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook yayin da yake mayar da martani ga kalaman Mike Arnold, wanda ya dade yana magana kan zargin gallazawa Kiristoci a Najeriya.
Martanin Sheikh Gumi ga Arnold
Arnold ya wallafa wasu hotuna a shafinsa na Facebook tare da manyan ‘yan Najeriya daga ciki har da tsohon gwamnan jihar Cross River, Donald Duke, da kuma ministan yaɗa labarai na Najeriya, Mohammed Idris.
Yayin wallafa hotunan, Arnold ya ce:
“Waɗannan kaɗan ne daga cikin mutanen da na haɗu da su da wuraren da na ziyarta a Najeriya cikin shekaru da suka wuce.”
Sai dai Gumi ya zargi Arnold da yaɗa abin da ya kira labarin ƙarya dangane da batun cewa ana yi wa kiristoci kisan kare dangi a Najeriya.
Sheikh Gumi ya zargi Amurka da ta'addanci
Malamin ya ce abin kunya ne Arnold ya zagaya wuraren da Kiristoci ke rayuwa cikin walwala amma bai kai ziyara jihohin arewa maso yamma da ke fama da matsalar tsaro ba.

Source: Facebook
A cewar Gumi:
“Bayan duk wannan surutan da ake yi kan ‘kisan kare dangi na Kiristoci na bogi’, abin kunya ne a gane cewa wannan mutum ya kusan kai ziyara ko'ina inda kiristoci ke rayuwa a cikin kwanciyar hankali da samun ci gaba, amma bai ziyarci Zamfara da Katsina da sauran jihohin Arewa da ke fama da ayyukan ‘yan bindiga da Boko Haram da ake zargin hukumomin leƙen asirin Amurka ne ke ɗaukar nauyinsu ba. Ɗaya daga cikin abubuwan da Musulunci ya tsana shi ne ƙarya da maƙaryata.”
Gumi ya magantu kan harin sojoji
A baya, kun samu labarin cewa fitaccen Malamin addinin Musulunci, Sheikh Ahmad Gumi ya buƙaci Majalisar Dattawa ta shiga batun yawan kai hare-hare da sojoji kan fararen hula a sassan Najeriya.
Ya ce ta’aziyya kaɗai ba ta wadatar ba, ganin yadda yanzu lamarin kai hari bisa kuskure ke neman zama ruwan dare a wasu daga cikin jihohin Najeriya ba tare da an dauki wani kwakkwaran mataki ba.
Rahotanni sun ce wani sabon hari da sojojin suka kai bisa kuskure kan wata kasuwa da ke iyakar Borno da Yobe ya kashe mutum 200, sai dai gwamnati ta bayyana cewa dama an rufe kasuwar tuntuni.
Asali: Legit.ng
