Masu Neman Takara 6 Sun Hakura, an Bar wa Shekarau Tikitin Sanatan Kano Ta Tsakiya
- Masu neman takara shida na jam’iyyar APC sun janye daga neman tikitin Sanatan Kano ta Tsakiya domin mara wa Malam Ibrahim Shekarau baya
- An cimma matsayar ne bayan wani dogon zaman tattauna wa domin fahimtar juna da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya jagoranta a Abuja
- Masu neman takarar sun ce sun bayyana dalilan da ya sa suka hakura da burin da suka sanya a gaba yayin da harkokin siyasa ke kara zafi a Najeriya
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Wasu masu neman takara shida na jam’iyyar APC sun janye daga neman tikitin kujerar Sanatan Kano ta Tsakiya gabanin babban zaɓen shekarar 202.
Dukkanin 'yan takarar da suka halarci taron sun sanar da cewa sun hakura, tare da bayyana goyon bayansu ga tsohon gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau.

Source: Facebook
Jaridar Channels ta ruwaito cewa an cimma matsayar ne a wani babban taro da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya jagoranta a birnin Abuja ranar Lahadi 10 ga watan Mayu, 2026.
Kano: An cimma matsaya kan takarar sanata
Jaridar Punch ta wallafa cewa rahotanni sun nuna cewa taron ya ɗauki sa’o’i da dama ana tattaunawa kafin ɓangarorin suka amince da matsayar da aka cimma ta tsarin maslaha.
Wadanda suka janye sun hada da Usman Bala, Sha’aban Sharada, Muhammad Zango, Danyaro Yakasai, Abbas Sani Abbas da Shehu Isa Driver.
Yayin da suke zanta wa da manema labarai bayan kammala taron, masu neman takarar sun ce sun janye takararsu ne domin zaman lafiya da haɗin kai a jihar Kano.
A cewarsu, mara wa Shekarau baya wani ɓangare ne na ƙoƙarin tabbatar da daidaito da kwanciyar hankali a siyasar jihar yayin da ake tunkarar zaɓen 2027.
Shekarau ya samu goyon baya
A watan Afrilu, 2026 ne Malam Ibrahim Shekarau ya fice daga jam’iyyar PDP tare da komawa APC bayan shafe lokaci yana nazarin makomarsa ta siyasa.

Source: Facebook
Tsohon gwamnan ya sanar da sauya shekar tasa ne a gidansa da ke Kano tare da wani jigo na PDP, Sanata Bello Gwarzo, yayin wani taro da magoya baya da mabiyansa suka halarta.
Da yake jawabi a wajen taron, Shekarau ya bayyana cewa ya ɗauki matakin ne bayan nazari mai zurfi kan zaɓuɓɓukan siyasa da suke gabansa.
Malam Ibrahim Shekarau ya taba zama gwamnan jihar Kano daga shekarar 2003 zuwa 2011. Haka kuma ya riƙe muƙamin ministan ilimi na tarayya tsakanin shekarar 2014 zuwa 2015.
APC ta tantance gwamnan Kano
A wani labarin kun ji cewa
Asali: Legit.ng

