Sojan Isra'ila Ya Sa wa Mutum Mutumin Mamar Yesu Sigari a Baki, Poland Ta Magantu

Sojan Isra'ila Ya Sa wa Mutum Mutumin Mamar Yesu Sigari a Baki, Poland Ta Magantu

  • Kasar Poland ta fusata kan yadda wani sojan kasar Isra'ila ya wulakanta mutum mutumin mamar Yesu Almasihu a wani yanki na Lebanon
  • Poland da ke da yawan Kiristoci mabiya Katolika ta yi Allah wadai da lamarin tare da cewa ba za ta lamunci cin mutunci irin wannan ba
  • A makon nan ne dai hoton wani sojan Isra'ila ya bayyana yana sanya wa mutum mutumin mamar Yesu Almasihu taba a baki a wani kauye

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Poland - Ma’aikatar harkokin wajen Poland ta ce ta fusata matuƙa bayan wani hoto ya bayyana a kafafen sada zumunta yana nuna wani sojan Isra'ila yana saka sigari a bakin mutum-mutumin mamar Yesu a Lebanon.

Kasar Isra'ila ta tabbatar da faruwar lamarin bayan shan suka daga kasashen duniya, inda ta ce za ta yi bincike domin daukar mataki.

Kara karanta wannan

Shin da gaske 'yan bindiga sun kashe mutane a wurin jana'iza a Plateau? Gaskiya ta bayyana

Sojan Isra'ila a kasar Lebanon
Sojan Isra'ila na na sa wa mutum mutumin mamar Yesu sigari a baki. Hoto: Middle East Mirror
Source: Facebook

Poland ta caccaki Isra'ila

Poland ta yi Allah wadai da lamarin a cikin wata sanarwa da ta fitar a X a ranar Alhamis, tana cewa ta lura cikin fushi da wani sabon lamari na sojan rundunar tsaron Isra’ila (IDF) yana cin mutuncin addini a Lebanon.

“Rainin hankalin da ya yi wa mutum-mutumin mamar Yesu ya ɓata ran Kiristoci,”

In ji sanarwar.

Hoton, wanda ya bazu sosai a kafafen sada zumunta ranar Laraba, an ɗauke shi ne a ƙauyen Debel da ke Kudancin Lebanon, wanda yawancin mazaunansa Kiristoci ne.

Wani hoton daban daga yankin ya bayyana a watan Afrilun 2026 yana nuna wani sojan Isra’ila yana dukan mutum-mutumin Yesu da guduma.

Ma’aikatar harkokin wajen Isra’ila ta ce an ɗauki sabon hoton ne makonni da suka gabata kuma za a ɗauki mataki kan sojan bayan binciken da aka gudanar kan lamarin.

Karin korafin Poland kan Isra'ila

Ma’aikatar harkokin wajen Poland da aka fi sani da bin Darikar Katolika sosai ta nuna cewa lamura biyu na iya zama rashin girmama batun kare haƙƙin ɗan Adam ta Majalisar Ɗinkin Duniya, wadda ke kare ‘yancin addini.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun nuna rashin imani, sun bude wa mutane wuta a wurin jana'iza a Filato

Rahoton Middle East Monitor ya ce ministan harkokin wajen Poland, Radosław Sikorski, ya ce sojojin IDF:

“Na buƙatar horo kan girmama sauran addinai da al’adu,”

Ya kuma yin Allah wadai da yawan waɗanda suka mutu a Gaza da kuma abin da ya kira wuce gona da iri da Yahudawa ke yi a West Bank.

Shugaban kasar Poland, Karol Nawrocki
Shugaban Poland, Karol Nawrocki na bayani a wani taro. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Isra’ila ta fara kai hare-hare a Kudancin Lebanon a watan Maris 2026 da manufar rusa ƙungiyar Hezbollah mai samun goyon bayan Iran.

Faransa ta yi korafi kan Isra'ila

A wani labarin, kun ji cewa gwamnatin kasar Faransa ta yi korafi game da yadda ake cigaba da cin zarafin mabiya addinin Kirista a Isra'ila.

Ma'aikatar harkokin wajen Faransa ta yi magana ne bayan an hango wani dan Isra'ila yana dukan wata mata mai hidima a wani coci.

Lura da cewa matar da aka yi wa duka 'yar kasar Faransa ce, gwamnatin Emmanuel Macron ta bukaci kama mutumin da hukunta shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng