Gwamnan Katsina ya nuna rashin tabbass kan biyan mafi karancin albashi N30,000

Gwamnan Katsina ya nuna rashin tabbass kan biyan mafi karancin albashi N30,000

- Gwamna Masari na jihar Katsina yace ba zai iya yanke hukunci ba a yanzu kan ko zai biya N30,000 mafi karancin albashi

- Gwamnan na Katsina ya fadi hakan a gangamin ranar ma’aikata a jihar

- Sai dai kuma Masari yace gwamnatinsa ta dauki jin dadin ma’aikata da matukar muhimmanci sosai

Gwamna Aminu Masari na jihar Katsina a ranar Laraba, 1 ga watan Mayu yace ba zai iya yanke hukuncin cewa ko zai biya ko kuma ba zai biya N30,000, sabon mafi karancin albashin ma’aikata ba.

Gwamna Masari, wanda ya samu wakilcin Shugaban ma’aikata Idris a gangamin ranar ma’aikata a Katsina, yace gwamnatinsa za ta gana da kungiyar kwadago akan lamarin, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Sai dai kuma yace, gwamnatinsa ta dauki jin dadin ma’aikata da matukar muhimmanci sosai.

Gwamnan Katsina ya nuna rashin tabbass kan biyan mafi karancin albashi N30,000
Gwamnan Katsina ya nuna rashin tabbass kan biyan mafi karancin albashi N30,000
Asali: Facebook

Shugaban kungiyar kwadago, Hussaini Hamisu, ya bukaci ma’aikata da su kwantar da hankalinsu yayinda kungiyar za ta tattauna da gwamnatin jihar kan sabon mafi karancin albashi.

KU KARANTA KUMA: El-Rufai da Fayemi na tseren neman kujerar Yari na Shugaban kungiyar Gwamnoni

Yayi korafin cewa rashin tsaro a jihar ya yawaita, inda ya bukaci ma’aikata da su jajirce wajen yin adda’a. Ya kuma yi alkawarin neman gwamnatin ta samar da Karin dabaru wajen magance matsalar rashin tsaro a jihar.

A halin da ake ciki, Legit.ng ta rahoto a baya cewa, Gwamna Abdul’aziz Yari na jihar Zamfara a jiya Laraba, 1 ga watanMayu yace shine zai zamo gwamna na farko a kasar da zai fara biyan N30,000, sabon mafi karancin albashi.

Da yake Magana a bikin ranar ma’aikata a garin Gusau, Yari ya gargadi ma’aikata akan sanya matayensu da yaransu a takardar biyan albashin.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel