Amurka Ta kai Harin ba Zata Iran, Trump Ya Yi Karin Haske kan Tsagaita Wuta

Amurka Ta kai Harin ba Zata Iran, Trump Ya Yi Karin Haske kan Tsagaita Wuta

  • Shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya yi magana bayan sojojinsa sun kai wani hari Iran duk da an yi yarjejeniyar tsagaita wuta
  • Donald Trump ya nuna cewa har yanzu alkawarin tsagaita wutar yana aiki, inda ya yi magana yana nuna cewa harin dan karami ne
  • A yanzu haka dai Iran ta sanar da kai har kan jiragen Amurka domin daukar fansa a kan farmaki ba zata da Donald Trump ya kai mata

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

America - Rahotanni sun nuna cewa shugaban Amurka, Donald Trump ya tabbatar da cewa sojojinsa sun kai hari kasar Iran a ranar Alhamis.

Trump ya bayyana cewa hare-haren da aka kai wa Iran sun biyo bayan harin da kasar ta kai hari kan jiragen ruwan yaƙin Amurka a mashigar ruwan Hormuz.

Kara karanta wannan

Ministan Iran ya je China, kasashen 2 sun ragargaji Amurka tare

Shugaba Donald Trump
Jiragen Amurka a hagu, Donald Trump a dama. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Al Jazeera ta rahoto cewa gwamnatin shugaba Donald Trump ta sanar da cewa bata tafka asara ba a harin da ta kai kasar Iran.

Maganar Donald Trump bayan harin Iran

Biyo bayan hare-haren Amurka a Iran, Trump ya bayyana shi a matsayin “ɗan ƙaramin hari,” yana mai cewa tsagaita wutar da ke tsakanin ƙasashen biyu har yanzu tana nan daram.

“Ɗan ƙaramin hari ne kawai,”

Trump ga Rachel Scott ta ABC News lokacin da aka tambaye shi game da harin.

Da aka tambaye shi ko musayar harin na nufin tsagaita wutar da ta fara aiki a watan da ya wuce, ta ƙare, Trump ya amsa da cewa:

“A’a, a’a, ana cigaba da tsagaita wutar. Har yanzu tana aiki.”

Trump ya yi wa Iran barazana

Daga baya Trump ya sake nanata barazanarsa cewa dole Iran ta amince da yarjejeniya domin a dawo tattaunawar kawo ƙarshen yaƙin, ko kuma ta sake fuskantar hare-hare.

Kara karanta wannan

Trump ya 'gano' raunin Iran a yakin Isra'ila, ya bukaci ta mika wuya

“Kamar yadda muka sake kai masu hari a yau, za mu ƙara kai masu hari mafi tsanani da tashin hankali a gaba idan ba su gaggauta sanya hannu kan yarjejeniyar ba!”

- Trump a wani sako da ya fitar.

Shugaba Donald Trump
Donald Trump dauke da bindiga yayin wata barazana ga Iran. Hoto: Getty Images
Source: Facebook

Rundunar sojin Amurka ta CENTCOM ta ce ta kai hare-hare Iran ne bayan Tehran ta harba makamai kan jiragen ruwan yaƙin Amurka da ke wucewa ta mashigar Hormuz.

“Sojojin Amurka sun dakile hare-haren Iran sannan suka mayar da martani ta hanyar hare-haren kare kai yayin da jiragen ruwan yaƙin Amurka masu makamai masu linzami ke ratsawa ta mashigar Hormuz zuwa Tekun Oman,”

In ji CENTCOM a wata sanarwa.

Iran ta farmaki sojojin Amurka

A wani labarin, mun kawo muku cewa rundunar sojin Iran (IRGC) ta sanar da kai harin ramuwar gayya kan wasu jiragen sojojin Amurka a kusa da mashigar Hormuz.

Iran ta ce ta kai hari kan jiragen ruwan yaƙin Amurka ne a matsayin martani ga hare-haren Amurka kan wani jirgin dakon man Iran da ke kan hanyar Hormuz.

Rundunar IRGC ta kuma yi iƙirarin cewa ta lalata jiragen ruwan yaƙin, tana cewa ta yi musu “babbar barna,” abin da gwamnatin Amurka ta nuna shakku a kai.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng