Jerin jihohin Arewa 9 da ake fuskantar matsanancin zafi

Jerin jihohin Arewa 9 da ake fuskantar matsanancin zafi

Da yawa daga cikin wasu yankunan Arewacin Najeriya na fuskantar matsanancin zafi da kuna ta dumamar rana cikin 'yan makonnin da suka gabata da a halin yanzu ake ci gaba da fargabar barkewar wasu nau'ikan cututtuka.

Ko shakka ba bu binciken manema labarai na jaridar Daily Trust ya tabbatar da cewa, jihohin Borno, Kano, Adamawa, Bauchi, Zamfara, Sakkwato, Katsina, Jigawa da kuma Kebbi, na cikin wani mawuyacin hali na rana zafi inuwa 'kuna.

Jerin jihohin Arewa 9 da ake fuskantar matsanancin zafi
Jerin jihohin Arewa 9 da ake fuskantar matsanancin zafi
Asali: Facebook

Hukumar kula da sauyin yanayi ta Najeriya NiMeT, ta yi hasashen cewa mawuyacin hali ba zai yanke ba domin kuwa za a ci gaba da fuskantar matsanancin zafi cikin yankunan na Arewa daga yanzu har zuwa watan Mayu a bana.

Masana kiwon lafiya sun bayyana cewa yanayi na zafi na tasirin gaske wajen barkewar annoba ta cututtukan Kwalara, Sankarau da sauran cututtukan fata masu nasaba da lokuta na zafi musamman maruru da kurajen zafi.

Binciken majiyar jaridar Legit.ng ya tabbatar da cewa, akwai rashin wutar lantarki da ya harzuka radadin yanayi na zafi da ake fama da shi a yankunan na Arewa. Hukumar NiMeT ta ce akwai rashin ruwan sha da kuma na gudanar da harkokin yau da kullum da ake fuskanta cikin jihohin na Arewa.

KARANTA KUMA: Tsadar Fulawa: Farashin Burodi zai tashi a Najeriya

A yayin da ake cin kasuwar ruwa da lemuka masu sanyi kamar ba bu gobe, da yawa daga cikin al'ummomin jihohin na Arewa sun kauracewa kwanciyar 'daka inda suke baje shimfidun su a fili yayin kwanciyar dare domin samun sauki na radadin zafi.

Domin kauracewa asarar dukiya, da dama daga cikin masu saye da sayarwar kayan gwari na dangin kayan itatuwa musamman tufa, inibi da kuma ayaba, sun gujewa sana'o'in su musamman a jihar Yobe da ke Arewa maso Gabashin Najeriya.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel