An kashe wasu ‘Yan bindiga a bakin fadar Sarkin Birnin Magaji

An kashe wasu ‘Yan bindiga a bakin fadar Sarkin Birnin Magaji

Jaridar Premium Times ta rahoto cewa Mutanen da ke cikin Garin Birnin Magaji a jihar Zamfara, sun kutsa har cikin fadar Sarkin Garin inda su ka gano wasu manyan ‘Yan bindiga har su ka hallaka su.

Kamar yadda labari ya zo mana, wadannan ‘yan bindiga su na cikin fadar Sarkin Garin ne inda ake wani zama na sulhu da su bayan an gano shanun jama'a a sakamakon hari da Dakarun sojojin Najeriya su ka kai cikin Dajin Birnin Magaji.

Kawo yanzu, sojojin saman Najeriya su na cigaba da luguden wuta a jihar Zamfara domin ganin bayan ‘Yan bindigan da su ka addabi Bayin Allah a jihar. A sakamakon wannan lugude, an fatattaki ‘yan bindiga da-dama da ke cikin daji.

KU KARANTA: An sace wani Basarake da ke kusa da Shugaban kasa a Daura

A farkon watan Afrilun da ya gabata ne aka fatattaki wadannan Miyagu daga cikin Dajin Birnin Magaji, inda bayan Sojoji da sauran jama’a sun shiga kungurmin Dajin, aka samu shanu fiye da 200 da wadannan ‘yan bindiga su ka sace.

A Ranar Larabar da ta gabata ne wasu daga cikin wannan ‘yan bindiga har su 7 da kuma wani jami’in tsaro na DSS su ka zo fadar Sarkin Birnin Magaji, Mai Martaba Husseini Dan Ali, domin ayi wani zama na neman sulhu da tsagaita wuta.

KU KARANTA: Abin da ya sa ake garkuwa da mutane a Najeriya

Bayan jama’a sun samu labarin wannan taro a fadar Sarkin ne su kayi maza su ka shiga har cikin gidan na mai martaba su ka rika lalube ko ta ina, sannan kuma su kayi kokarin cinnawa gidan wuta, har sai da ta kai wasu Sojoji sun tsoma baki.

Mutanen Garin sun jira wadannan ‘Yan bindiga har su ka fito daga cikin fadar da kan su, sannan su ka kashe su a take. A lokacin da wannan abu, Mai Marataba Sarki Husseini Dan-Ali, ba ya nan, sai dai aka samu Magatakardansa a cikin fadar.

Shi ma dai jami’in DSS na farin kaya da ke tare da wadannan ‘Yan bindiga ya sha ne da kyar da raunuka kaca-kaca bayan Sojoji sun kai masa dauki. Kawo yanzu Jami'an ‘yan sanda ba su ce komai ba tukun.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Mailfire view pixel