Firai Ministan Birtaniya ta sallami Ministan tsaro

Firai Ministan Birtaniya ta sallami Ministan tsaro

Firai Ministar kasar Birtaniya Theresa May, a ranar Laraba ta fatattakin babban sakataren tsaro na gwamnatin kasa, Gavin Williamson, sakamakon takaddamar bayyanar wani rahoton sirri akan inganta harkokin sadarwar zamani na kasar.

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa, an samu bayyanar wani rahoton sirri da gwamnatin kasar Birtaniya da kulla yarjejeniya da kamfanin Huawei na ksar Sin domin samar da ingancin harkokin ta na sadarwar zamani na 5G Network.

Firai Ministan Birtaniya, Theresa May
Firai Ministan Birtaniya, Theresa May
Asali: UGC

Kamar yadda rahotanni suka bayyana, Firai Minista Theresa a Yammacin Laraba ta nemi Ministan tsaro na kasar Birtaniya da ya ajiye aikin sa sakamakon rashin yarda da kuma rashi na aminci da ya shiga tsakanin su a yanzu.

Yayin barrantar da shi daga majalisar ta, Theresa ta ce ba bu aminci na danka ragamar harkokin tsaron kasar Birtaniya a hannun Mista Williamson kamar yadda kakakin fadar gwamnatin ta da ke ofishin Downing ta bayyana.

Theresa cikin yakini ta tabbatar da cewa, Ma'aikatar tsaro karkashin jagorancin Mista Gavin ke da alhakin bayyana rahotannin sirri da suka tattauna yayin taron tsaro na kasar da aka gudanar a ranar 23 ga watan Afrilu.

KARANTA KUMA: Garkuwa da Mutane: IG na kasa ya sauya Kwamishinan 'yan sandan jihar Kaduna

Rahotanni daga fadar gwamnatin kasar Birtaniya da ke yankin Downing a birnin Ingila sun bayyana cewa, Ministan Mata da daidaito, Penny Mordaunt, za ta karbi ragamar jagorancin ma'aikatar tsaro a matsayin Mace ta farko da za ta rike wannan kujera yayin ci gaba da rike tsohon mukamin ta.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel