Latest
A yayin da za a fafata tsakanin Najeriya da kasar Algeria a zagaye na biyun karshe na gasar kofin nahiyyar Afirka AFCON, shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmed Lawan, ya jagoranci tawagar gwamnatin Najeriya zuwa kasar Masar.
Wani tsohon Soja ya sha alwashin ganin bayan Boko Haram idan a ka kira sa ya bada shawara. Sojan ya ce idan a ka kira mu filin daga, za mu gama da Boko Haram a watanni uku.
Tsohon minista kuma tsohon shugaban kungiyar dattawan Arewa, Paul Unongo, ya yi hasashe tare da kyautata zato a kan Arewacin Najeriya wajen samar da shugaban kasa tare da ci gaba da rike akalar jagoranci a zaben 2023.
Usman Shehu, tsohon da jarida ne da ya taba aiki da sashen Hausa na radiyon Amurka (VON) da gidan radiyon jihar Bauchi (BRC), yanzu haka kuma shine babban editan sashen Hausa na gidan radiyon Duetsche Welle (DW) da ke kasar Jamus.
Mutane biyar da suka hadar da wata sabuwar amarya sun yi gamo da ajali yayin da kimanin mutane 14 suka jikkata a wani mummunar hatsarin mota da ya auku a kauyen Akila dake babbar hanyar Abeokuta zuwa Ibadan ta jihar Ogun.
Tabbas rayukan mutane 10 sun salwanta kamar yadda hukumomin tsaro suka bayyana a sakamakon wani mummunan hari na 'yan daban daji da ya auku a kauyen Kirtawa na karamar hukumar Safana ta jihar Katsina.
Fitacce kuma mafi shaharar jaruman fina-finan Hausa na dandalin Kannywood, Ali Nuhu, ya yi karin haske dangane da dalilai da suka sanya shamaki a tsakanin shirin fina-finan Arewa da kuma na Kudancin kasar nan.
Matar ta sa mai suna Ronke, a cewar Hakeem tana ha’intarsa a cikin zamantakewarsu ne ta aure. Hakeem ya antayo wannan jawabin ne gaban alkalin kotun, Ademola Odunade a sanadiyar kararsa da matar ta kai na cewa ya na nuna mata uqub
Hukumar hana fasa kauri ta kasa ta yi gargadin cewa, kwantenoni shida cike makil da nikakken tumatir mai dauke da guba ya shigo Najeriya daga kasar Iran da aka killace shi da sunan 'Shirin Asal my tomato paste'.
Masu zafi
Samu kari