Rundunar Sojan kasa ta sauya ma manyan janarori mukamai daban daban

Rundunar Sojan kasa ta sauya ma manyan janarori mukamai daban daban

Rundunar Sojan kasa ta gudanar da wasu sauye sauye a mukaman wasu manyan janarorinta, kamar yadda babban hafsan sojan kasa, Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai ya amince.

Kaakakin rundunar, kanal Sagir Musa ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa daya fitar a ranar Lahadi, 14 ga watan Yuli, inda yace wadanda sauye sauyen ya shafa sun hada da Laftanar janar guda daya, Manjo janar – manjo janar da Birgediya birgediya da dama.

KU KARANTA: Dasuki: Jigo a APC ya bukaci Buhari ya bi umarnin kotu

Buratai ya sauya Laftanar janar L.O Adeosun mukami daga shugaban bada horo da aikace aikace zuwa shugaban tsare tsare na rundunar, yayin da aka dauke Majo Janar AO Shodunke daga shelkwatar sojan kasa zuwa shelkwatar tsaro a matsayin shugaban zirga zirga. Sauran sun hada da;

Manjo janar AA Tarfa zuwa mukamin kwamandan sashin manufofi dake Minna

Manjo janar EO Udoh sabon shugaban horo da ayyuka na rundunar

Manjo janar MS Yusuf shugaban mulki

Manjo janar JI Unuigbe shugaban zirga zirga na rundunar

Manjo janar OF Azinta shugaban tabbatar da kididdigan ingancin tsari

Manjo janar AB Omozoje sabon kwamandan runduna ta 2 dake Ibadan

Manjo janar AB Biu is sabon kwamandan runduna ta 7 dake Maiduguri

Manjo janar JJ Ogunlade sabon kwamandan runduna ta 8 dake Sakkwato

Manjo janar JO Irefin sabon kwamandan runduna ta 81 dake Legas

Manjo janar KAY Isiyaku sabon kwamandan Sojojin shelkwatar tsaro Abuja

Manjo janar AA Jidda shugaban aikin tabbatar da tsaro a kasashen waje

Manjo janar JO Oni daraktan saye saye a shelkwatar tsaro

Manjo janar OA Akintade sabon kwamanda ordinance dake Legas

Manjo janar OW Ali darakta cibiyar horaswa ta Sojan kasa dake Zaria

Manjo janar EN Njoku daraktan watsa labaru

Manjo janar CG Musa kwamandan shiyya ta 3 na Lafiya dole dake Monguno

Manjo janar OT Akinjobi ya koma shelkwatar tsaro.

Sauran wadanda sauyin ya shafa sun hada da Brig Gen KA Kazir, Brig Gen AE Attu, Brig Gen MT Usman, Brig Gen UT Musa, Brig Gen GO Adesina, Brig Gen LA Fejokwu, Brig Gen EAP Undiandeye, Brig Gen JY Nimyel, Brig Gen OO Oluyede, Brig Gen PP Malla, Brig Gen OM Bello, Brig Gen MA Etsu-Ndagi, Col RC Emeh, Col MO Erebulu, Lt Col SA Abimbola da kuma Lt Col SM Ahmed.

Daga karshe Buratai ya taya Sojojin murna, tare da yi musu fatan alheri, sa’annan ya shawarcesu dasu jajirce wajen gudanar da ayyukansu a sabbin mukamansu tare da yin biyayya ga dokokin Najeriya.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel