'Yan wasan Arewa ba su son fitowa a fina-finan Kudu - Ali Nuhu

'Yan wasan Arewa ba su son fitowa a fina-finan Kudu - Ali Nuhu

Fitacce kuma mafi shaharar jaruman fina-finan Hausa na dandalin Kannywood, Ali Nuhu, ya yi karin haske dangane da dalilai da suka sanya shamaki a tsakanin shirin fina-finan Arewa da kuma na Kudancin kasar nan.

Kamar yadda jarumi Ali Nuhu ya zayyana, da yawa daga cikin 'yan wasan Arewa su kan kauracewa fitowa a fina-finan Kudancin kasar nan a sakamakon bambancin akidar addini da kuma al'adu.

Sau da dama fina-finan Kudancin Najeriya su kan yi matashiya tare da bayyana akidu na al'adun Yarbawa, Igbo da makamantan su tare da akidar tsarin addinin Kirista. Hakan ya sanya 'yan wasan kwaikwayo na Arewa ke gaza taka rawar gani a wannan fina-finai da suka sabawa dabi'un su.

Ali Nuhu yake cewa, kowa ne jarumi ya kan yi iyaka bakin kokarin sa wajen tabbatar da isar da sako daidai da tsari na addini da kuma al'ada ga masu kallo. Wannan na daya daga cikin manyan dalilai da suka sanya 'yan wasan Arewa ke kauracewa fina-finan Kudancin Najeriya.

KARANTA KUMA: Nikakken tumatir mai dauke da guba ya shigo Najeriya daga kasar Iran - Hukumar Kastam

Ya ci gaba da cewa, sabanin yadda ake ikirarin akwai tsauri a kamfanin shirya fina-finai na Arewa, Ali Nuhu ya ce ba bu yadda za a yi wani jarumi ko kuma wata jaruma ta bayyana a cikin kowane nau'i na wasan kwaikwayo da ya sabawa akidar musulunci da kuma al'adun Arewa.

Bugu da kari, a yayin da hakan ya kasance wani bigire na nuna kwarewa a kan sana'a, 'yan wasan kwaikwayo na da burin fitowa a nau'ikan fina-finai daidai da bukata da kuma muradin masoya masu kallon su.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel